Lewandowski na gaba a cin kwallaye a La Liga da kai hare-hare

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Robert Lewandowski shine kan gaba a cin kwallaye a La Liga kawo yanzu a kakar bana mai 15 a raga.

Haka kuma tsohon dan kwallon Bayern Munich, shine kan gaba a yawan kai hare-haren cin kwallo a babbar gasar ta Sifaniya mai 41.

Ranar Asabar za a ci gaba da wasannin La Liga karawar mako na 28, bayan an kammala fafatawa tsakanin kasa da kasa a ranakun da Fifa kan ware.

Tun bayan da dan kwallon Poland ya koma Sifaniya da taka leda kan fara gasar bana, Xavi ke anfani da shi a gurbin mai cin kwallo, sai idan ya ji rauni.

Kenan a yawan hare-haren da Lewandowski kan kai a La Liga ya ci kwallo kaso 36.6 cikin 100 kenan.

Shi kuwa dan wasan Real Madrid Karim Benzema, wanda ya lashe kyautar yawan cin kwallaye a bara, ya kai hari sau 30 da zura kwallo 11 a raga.

Shima dan wasan Real Madrid, Vinicius Junior hari 30 ya kai amma kwallo takwas ya ci kawo yanzu a La Liga.

Enes Unal na Getafe, shine na biyu a yawan cin kwallaye a La Liga mai 13, amma hari 28 ya kai a raga kawo yanzu.

Kenan a kaso 46.4 da dan wasan Getafe ya kai hare-haren, shine ya zura kwallo 13 a raga.

A manyan gasar Turai biyar, Lewandowski shine na shida a jerin 'yan kwallon da ke gaba a kai hare-haren cin kwallaye.

Kylian Mbappe ne kan gaba wanda ya kai hari 58 da Leo Messi mai 46 dukkansu daga Paris St Germain.

Harry Kane na Tottenham shine na uku, wanda ya kai hari 46 da Erling Haaland na Manchester City mai 44 da kuma Jonathan David na Lille mai 4).

'Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga a bana:

  • Robert Lewandowski Barcelona 15
  • Enes Unal Getafe 13
  • Iago Aspas Celta de Vigo 12
  • Borja Iglesias Real Betis 12
  • Joselu Espanyol 12
  • Karim Benzema Real Madrid 11
  • Alvaro Morata Atletico de Madrid 10
  • Vedat Muriqi Real Mallorca 10
  • Alexander Sorloth Real Sociedad 9
  • Gabriel Veiga Celta de Vigo 9
  • Antoine Griezmann Atletico Madrid 9

Kawo yanzu bayan wasa 26 a La Liga, Barcelona ce ta daya a kan teburi da maki 68, sai Real Madrid ta biyu mai maki 56 da kuma Atletico Madrid mai maki 51.

Wasannin mako na 27 da za a ci gaba da buga wa a karshen mako:

Ranar Juma'a 31 ga watan Maris

  • Real Mallorca da Osasuna

Ranar Asabar 1 ga watan Afirilu

  • Girona da Espanyol
  • Athletic Bilbao da Getafe
  • Cadiz da Sevilla
  • Elche da Barcelona

Ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu

  • Celta Vigo da Almeria
  • Real Madrid da Real Valladolid
  • Villarreal da Real Sociedad
  • Atletico Madrid da Real Betis

Ranar Litinin 3 ga watan Afirilu

  • Valencia da Rayo Vallecano