Liverpool ta ci wasan farko a Champions League na bana

Liverpool

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool ta yi nasarar doke Ajax da ci 2-1 a wasa na biyu a cikin rukuni a Champions League da suka fafata a Anfield ranar Talata.

Mohamed Salah ne ya fara ci wa Liverpool kwallo a minti na 17 da take leda, minti 10 tsakani Ajax ta farke ta hannun Mohammed Kudus.

Joel Matip ne ya ci wa Liverpool kwallo na biyu da ya bai wa kungiyar damar lashe wasan farko a kakar bana a Champions League.

Daman Jurgen Klopp ya bukaci 'yan wasa da su saka kaimi, bayan da Napoli ta doke Liverpool 4-1 a wasan farko a rukunin farko a makon jiya.

Liverpool ta samu damarmaki da yawa, shi ne har ta kai kungiyar Anfield ta ci kwallon farko.

Ita kanta Ajax, wadda ta doke Rangers 4-0 a makon jiya ta zubar da damarmaki da yawa.

Wasannin da aka kara tsakanin Liverpool da Ajax:

2022/23

Champions League Talata 13 ga watan Satumbar 2022

  • Liverpool 2-1 Ajax

2020/2021

Champions League Talata 1 ga Disambar 2020    

  • Liverpool         1 - 0     Ajax

Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 2020   

  • Ajax     0 - 1     Liverpool         

1966/1967

European Cup Laraba 14 ga watan Disambar 1966         

  • Liverpool         2 - 2     Ajax    

European Cup          We 07Dec 1966         

  • Ajax     5 - 1     Liverpool