Kulob uku na Turkiyya na son Trippier, West Ham na son Matip

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kieran Trippier
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Kungiyoyin Fenerbahce, da Besiktas da kuma Eyupspor na son daukar dan wasan Newcastle Kieran Trippier bayan kokarin da kungiyar Al-Ittihad ta Saudi Pro-League ta so daukar dan wasan mai shekara 33, kuma tsohon mai taka leda a Ingila. (Sky Sports)

West Ham na son tsohon dan wasan Kamaru Joel Matip,mai shekara 33, da dan wasan jamhuriyar Ireland John Egan, mai shekara 31, daidai lokacin da suke neman sabon dan wasan baya a kulub din.(Sky Sports)

Da wuya Manchester United ta bar dan wasan tsakiya na Denmark Christian Eriksen mai shekara 33 barin kungiyar a watan nan (Football Insider)

Newcastle za ta kara kokarin sake dauko dan wasan Swedin mai taka leda a Nottingham Forest Anthony Elanga nai shekara 22 idan an bude kasuwar musayar 'yan wasa (Football Insider)

Ajax ta amince da bada aron dan wasan gaba na Ghana Kamaldeen Sulaiman mai shekara 22 ga kungiyar Southampton. (Fabrizio Romano)

Liverpool da Arsenal na daga cikin masu zawarcin matashin dan wasan baya na Brazil Voctor Reis mai shekara 18. (Caughtoffside)

Everton ta tankwabe tayin dan wasan Chelsea Axel Disasi, dan wasan Faransar mai shekara 26, ta kuma tankwabe dauko dan wasan gaba na Ivory Coast David Datro Fofana, 21, domin maye gurbin dan wasan Ingila Dominic Calvert-Lewin, 27. (Givemesport)

Dan wasan Manchester City, Joe Ndala mai shekara 18 ya na gwajin lafiya, kafin komawa kungiyar PSV a matsayin bashi, da kuma yarjejeniyar sayan dan wasan nan gaba. (Athletic - subscription required)

Dan wasan gaba na Romania Ianis Hagi, 25, ya shirya tsaf domin watsi da batun ficewa daga kungiyar zuwa Bucharest side FCSB. (Football Insider)