Arteta ya tsawaita kwantiraginsa da Arsenal

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya amince da sabon kwantiragin shekara uku da ƙungiyar ta arewacin Landan.

Kwantiragin ɗan ƙasar Sifaniyan dai na shirin ƙarewa ne a ƙarshen kakar wasa ta bana amma yanzu ana sa ran zai ci gaba da zama har zuwa shekarar 2027.

Gunners ta naɗa Arteta, wanda ya kasance koci a ƙarƙashin Pep Guardiola a Manchester City a lokacin, don maye gurbin Unai Emery a matsayin koci a watan Disamban 2019.

Ya jagoranci Arsenal ta samu nasara a wasan ƙarshe na cin kofin FA a ƙarshen kakar wasa ta 2019-2020 inda ya lashe kofinsa na farko a matsayin koci.

Ana sa ran za a tabbatar da sabuwar yarjejeniyar Arteta kafin wasan hamayyar arewacin London da za a yi ranar Lahadi mai zuwa a filin wasan Tottenham.

Bayan wasanni uku a bana Arsenal ce ta huɗu a teburin gasar Premier, inda ta yi nasara a wasanni biyun farko da Wolves da Aston Villa kafin ta yi kunnen doki da Brighton.

Tsohon ɗan wasan tsakiya, Arteta ya buga wa Gunners wasanni 150 a lokacin da yake buga wasa har ya kai ga ya zama kyaftin ɗin ƙungiyar.