Utd da City na gogayya kan Frimpong, Gomes na ɗaukar hankalin ƙungiyoyi

Asalin hoton, SNS GROUP
Manchester United da Manchester City na matuƙar son gwanin ɗan wasan Bayer Leverkusen da Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 23. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Ingila Angel Gomes, mai shekara 24, na ɗaukar hankalin ƙungiyoyin gasar Premier da wasu na Turai, abin da ya sa har ma ƙungiyarsa Lille ke shirin karɓar tayi a kan ɗan wasan da ya kasance renon cibiyar horad da matasan ’yan ƙwallo ta Manchester United. (Telegraph)
Newcastle United za ta fuskanci gogayya daga Liverpool da Manchester United idan har ta sake gabatar da tayin sayen ɗan bayan Ingila Marc Guehi, na Crystal Palace a watan Janairu. (Football Insider)
Manchester City na duba yuwuwar sayo ɗan wasan tsakiya na Torino Samuele Ricci, na Italiya mai shekara 23, domin ya maye gurbin Rodri na Sifaniya wanda ya ji rauni. (Guardian)
Liverpool na shirin ƙara yawan ƴan wasanta masu kai hari a 2025, inda take harin sayen ɗan wasan gaba na gefe na Borussia Dortmund Karim Adeyemi, na Jamus mai shekara 22. (Teamtalk)
Ɗan wasan gaba na gefe Anthony Gordon, mai shekara 23, na dab da sanya hannu a wani sabon kwantiragi na shekara shida da Newcastle, wanda hakan ba zai yi wa Liverpool da ke sonshi ba daɗi. (Mirror)
Liverpool ɗin tana kuma son ɗan wasan tsakiya na Freiburg Merlin Rohl, mai shekara 22, wanda ya taka wa Jamus leda a tawagarta ta ƴan ƙasa da shekara 21. (Bild)
Arsenal ba ta da niyyar sayar da Takehiro Tomiyasu, mai sheakara 25, duk da alakanta ɗan bayan na Japan da ake yi da tafiya Inter Milan a watan Janairu.
Barcelona ta yarda ta biya tsohon ɗan wasan da Manchester United take so Frenkie de Jong albashinsa da ta da ɗage biya - wanda ya kai yuro miliyan 18 (£15m) - bisa sharaɗin cewa ɗan wasan na tsakiya na Netherlands, ya yarda ya bar ƙungiyar a bazara mai zuwa. (FootballTransfers)
Manchester United ta samu amincewar hukumar gasar Premier, kan sayen matashin ɗan wasan gaba na Arsenal, Chido Obi-Martin, ɗan Denmark mai shekara 16. (Manchester Evening News)
An gaya wa Wolves cewa sai ta tanadi fam miliyan 40, idan har tana son matashin ɗan wasan gaba na gefe na Burnley da tawagar Italiya ta ƴan ƙasa da shekara 2, Luca Koleosho, mai shekara 20, wanda Nottingham Forest da Newcastle ma suke so. (Football Insider)
Ɗan wasan tsakiya na Arsenal Jorginho, na Italiya mai shekara 32, na tunanin komawa aikin horad da ƴan wasa a Gunners ɗin idan kwantiraginsa ya ƙare a 2025. (FootballTransfers)










