Takunkumai sun jefa ƴan Nijar cikin 'mawuyacin hali'

    • Marubuci, Chris Ewokor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC, Abuja
    • Marubuci, Tchima Issoufou
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC, Niamey
  • An wallafa

Yana zaune a ƙofar shagonsa na magani a Yamai, Abdourahamane Id cikin farin ciki ya hango wani ya nufo shagon, yana tunanin ya samu kwastoma, amma ba yadda ya so ba, ashe ɗan jarida ne.

Da yake bayyana girman yadda kasuwanci ya gurgunce, ɗan kasuwar mai shekara 25 daga Maradi ya nuna yadda shagonsa ya kusan komawa ba komai a ciki

“So da dama mutane kan zo shago na sayen magani da aka rubuta ma su daga asibiti, amma yanzu ba kuɗi"

Ya ce tun juyin mulkin da sojoji suka yi, rayuwa ta sauya sosai.

Wane tasiri ne takunkuman suka yi?

Nijar mai yawan al'umma miliyan 27 na ƙoƙarin shawo kan mummunan tasirin takunkuman.

A watan Yuli, wasu ƙasashen yammacin Afirka maƙwabtan Nijar suka ƙaƙaba wa ƙasar takunkumi saboda juyin mulkin - inda suka taƙaita cinikayya da katse lantarki da kuma hada-hadar kuɗi.

Shugabannin ƙasashen sun ɗauki matakin ne domin hana sake faruwar juyin mulki a yankin sahel.

Tun 2020, juyin mulki shida aka yi a yammacin Afrika.

Takunkuman da suka samu goyon bayan Tarayyar Turai sun kasance masu tsauri da aka ƙaƙaba wa wata ƙasa mamba a ƙungiyar Ecowas.

Da farko Najeriya da Benin ne suka fara rufe kan iyakoki, daga nan Najeriya ta sake katse wa Nijar lantarki. Sannan an dakatar da hada-hadar kuɗi tsakanin Nijar da wasu kasashen yammacin Afirka.

Kafin juyin mulkin, kasafin kuɗin Nijar na dogaro ne kacokan da tallafin da ƙasar ke samu daga waje. Amma daga baya Faransa da Amurka (da ke ba nijar tallafin lafiya da tsaro da wasu buƙatunta) sun sanar da dakatar da tallafin.

Watanni biyar bayan hamɓarar da shugaba Bazoum, al'ummar Nijar na ci gaba da kokawa kan tasirin takunkuman ga rayuwarsu ta yau da kullum.

Ƴan Nijar na shan wahala wajen samun kuɗaɗen da za su ciyar da iyali musamman manoma da makiyaya waɗanda suka fi dogaro da fitar da amfanin gona da dabbobi zuwa Najeriya.

Ƙasar na fuskantar barazanar ƙarancin abinci tun kafin juyin mulki. Kwanaki bayan juyin mulkin, hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta shigar da abinci ga mutum 140,000 a sassan ƙasar da kuma abinci mai gina jiki ga yara 74,000, kamar yadda hukumar WFP ta bayyana a lokacin da aƙalla kashi 13 na ƴan Nijar ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci.

Tun lokacin, hukumar WFP ta ce takunkuman da rufe kan iyakoki sun hana ci gaba da shigar da kayan abincin da magunguna cikin Nijar.

Hukumar ta bayyana damu kan girman tasirin takunkuman musamman tsadar kayan masarufi waɗanda suka ƙara nesanta abinci ga ƴan Nijar.

Baya ga kasancewar Najeriya babbar abokiyar hulɗar Nijar a bangaren cinikayyar kayan amfanon gona, ƙasar ita ce ke samar da Nijar kaso 70 na wutar lantarki kafin juyin mulkin. Kuma tun lokacin ƴan Nijar ke fuskantar matsalar makamashin.

‘Takunkumai sun gurgunta mu’

Jamila Amadou Garba mai shekara 49 kuma ƴar kasuwa, kuma matar aure wadda aka taɓa mutuwa aka bari da marayu, ta ce kula da ƴaƴanta bakwai yana neman ya gagara.

Kafin juyin mulkin, suna iya cin abinci sau uku a rana amma a yanzu sau ɗaya ma sai da ƙyar - wani lokaci shinkafa ko garin kwaki idan ya samu.

"Ina samun garin rogo, da sikari da mai mu haɗa da kuli kuli, muka ci haka don kada a zauna da yunwa."

A wurin, Allah ne kaɗai zai taimake su ci gaba da jure wannan wahala da aka shiga.

"Gaskiyar magana muna cikin mawuyacin hali domin waɗannan takunkuman sun gurgunta mu, mun rasa yadda za mu ji daɗin rayuwarmu," in ji ta.

Haka ma, Rafiou Habibo, ya ce watanni biyar da suka gabata abubuwa sun sauya matuƙa. Lokacin da ba takunkumi, muna sayen buhun shinkafa daga $13 zuwa $17, amma yanzu mai sauƙi ana samunta $25," in ji shi.

A Kasuwar Transat da ke Damagaram, Kabirou Souley Ousmane ya ce yana fatan abubuwa za su sauya. Yana sayar da kayan gine-gine kuma ya ce takunkuman sun hana kasuwa saboda ba kuɗi.

‘Ba su da kuɗin da za su biya’

Magunguna da suka kasance na buƙatar yau da kullum sun yi wahala. Kuma inda za a iya samu sun yi tsada.

A shagon magani, Abdourahamane ya ce masu shaguna da dama ba su iya samun kaya kuma ba kuɗi.

Suna ƙoƙarin samun kaya daga ƙasashen Chadi, a cewarsa.

"Mutane na zuwa wurinmu suna ƙorafi cewa ba su da isassun kuɗi suna zuwa neman rance wajenmu. Wasu har durƙusawa ƙasa suke suna roƙo. "Dibi shagon maganin nan ba komi a ciki."

Ya ƙara da cewa: "Muna matsalar magunguna da rashin kuɗi"

Ya yi iƙirarin cewa cututtuka da dama kamar zazzabin maleriya na kisan mutane.

Kusan rabin mace-mace a Nijar ana alaƙanta su ne da zazzabin maleriya, a cewar hukumomi.

Sojoji na lalaben mafita

A watan Nuwamba, shugaban Sojin Nijar Abdourahmane Tchiani ya kai ziyara makwabtan kasashen Mali da burkina Faso.

Ƙasashen na da muhimmanci. Baya ga makwabta, dukkanin ƙasashen suna ƙarƙashin mulkin soji. Sun ƙulla ƙawance ta tsaron juna - wani mataki tunkarar takunkumai.

Sun amince su yi aiki tare da ƙulla ƙawancen tattalin arziki da siyasa kuma sun sanar da matakan ƙarfafa cinikayya tsakaninsu inda suka amince kan ayyukan makamashi da masana'antu da samar da bankin saka jari da kamfanin jirgin sama na bai-ɗaya

Amma sojojin Nijar a Yamai na ci gaba da fuskantar matsin lamba.

Dukkanin ƙasashen na fuskantar barazanar hare-haren ƴan bindiga masu ɗa'awar jihadi.

Masana tsaro sun bayyana damuwa cewa takunkuman Nijar na iya yin cikas ga ƙoƙarin ƙasar na yaƙi da ƴan bindiga a sassan ƙasar.

Nijar na cikin rundunar tsaro ta MJTF da ta ƙunshi ƙasashen Benin da Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya da ke da shalkwata a N'Djamen, kuma an kafa rundunar ne da nufin kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram kuma har zuwa 2023 Nijar na nan a matsayin mamba.

Kodayake babu tabbaci a hukumance cewa ta fice, amma masana tsaro kamar Kabiru Adamu a Abuja ya shaida wa BBC cewa alamu sun nuna Nijar tana ja da baya.

An ƙaƙaba wa ƙasar takunkumai ne domin tilasta wa sojojin da suka ƙwaci mulki dawo da ƙasar turbar ɗimokuraɗiya, in ji Paul Ejime masanin harakokin Afirka a London, amma maimakon haka ƴan ƙasar ne ke shan wahala.

Dakatar da hada-hadar kuɗi da Ecowas ta yi musamman Bankin raya yammacin Afirka - na nufin kuɗi ba ya shiga, ya ce wannan babbar hasara ce ga ƙasa wadda kusan kasafin kuɗinta ya dogara ne da tallafin ƙasashen waje.

Ejime ya ƙara da cewa Nijar ba ita kaɗai ba ce ke wahala, matakin ya shafi Benin da Najeriya da Ghana saboda hana cinikayya. "Duk abin ya shafi ƙasa ɗaya zai shafi saura. Babban al'amari ne ga Ecowas," a cewarsa.