Abubuwan da ke janyo haihuwar jarirai masu matsalolin halitta
Matsalolin da suka shafi halittar jarirai sun kasu kashi biyu, wadanda ake iya gani a zahiri da kuma wadnda suka shafi yadda bangarorin jikin dan Adam ke aiki, in ji masana a fannin kiwon lafiya.
Sai dai likitoci sun ce mafiya yawan wadannan illoli ba a san abin da ke janyo su ba, amma kadan daga cikinsu suna da alaka da yanayin kwayoyin halitta suke.
Cututtuka kamar su noma da illoli da suka shafi halittar zuciya da haihuwar yaro da gurguntaka na daga cikin larurorin da ba a sana bin da ke janyo su ba a likitance.
Amma bincike ya nuna cewa wasu illolin halittar shan barasa ko taba sigari ne ke janyo su, wasu cututtuka ne, yayin da wasu kuma shakar sinadarai masu hatsari ne ke janyo su.
Alkaluman hukumar lafiya ta duniya sun nuna cewa akalla jarirai dubu 295 ne ke mutuwa a duk shekara a sakamakon wasu illoli na halitta da suka dauke da su.
Lamarin da ya fi kamari a kasashe masu matsakaici da kuma karancin kudin shiga.













