Arsenal ta mayar da hankali kan Declan Rice, Jude Bellingham yafi sha'awar Liverpool

An wallafa

Arsenal ta sa Declan Rice, dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila mai shekara 24 cikin 'yan wasan da suka fi bukata a karshen wannan kakar wasan, saboda da kamar wuya Gunners su iya samun fam miliyan 150 da ake bukata domin sayo Jude Bellingham, dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund mai shekara 19. (Football.London)

Sai dai Rice na iya komawa Liverpool, inda ake sa ran zai taimaka wajen sake gina kungiyar, kamar yadda tsohon dan wasan tsakiya na kungiyar Dietmar Hamann ya bayyana. (Talksport)

Kuma shi kansa Bellingham bai daina bayyana sha'awarsa ta komawa Liverpool ba duk da rashin karsashin da kungiyar ke nunawa a baya-bayan nan, kuma yana sha'awar aiki tare da kocin kungiyar Jurgen Klopp. (Athletic - subscription required)

Manchester United na son karfafa rukunin 'yan tsaron bayan kungiyar ta hanyar sayen dan wasan Napoli da Koriya ta Kudu Kim Min-jae mai shekara 26 wanda aka makala wa farashin fam miliyan 42. (Corriere dello Sport - in Italian)

A wani labarin kuma, United na sha'awar tsawaita zaman dan wasanta na gaba Alejandro Garnacho mai shekara 18. Dan kasan Argentinan zai iya barin United a 2024, amma kungiyar na son ya dade yana jan zarensa, shi yasa za ta yi masa tayin albashi mai tsoka. (Mail)

Da alama dan wasan tsakiya na Brazil Dabinho mai shekara 29 na kan hanyarsa ta ficewa daga Liverpool bayan da ya shafe shekara biyar a Anfield, domin Jurgen Klopp na shirin sake wa kungiyar garambawul. (Mirror)

Tottenham na kan gaba wajen zawarcin James Maddison, dan wasan tsakiya na Leicester City da Ingila mai shekara 26. (Football 365)

Dan wasan gaba na Belgium Romelu Lukaku mai shekara 29, ba ya dokin komawa Chelsea bayan da wa'adin da aka diba na aro da aka tura shi zuwa Inter Milan ke daf da karewa a karshen wannan kakar wasan. (90min)

Arsenal ta mika wani tayi na euro miliyan 70 ga Barcelona domin sayen Raphina, dan wasanta mai shekara 26 nan zuwa watan Janairu mai zuwa. (Sport - in Spanish)