Ranar Yara: Makarantar da malami daya ke koyarwa

An wallafa

Asusun kula da kananan yara na Majalaisar Dinkin Duniya, UNICEF ya ware duk ranar 27 ga watan Mayu domin tunatar da al’umma da gwamnatoci muhimmancin yara manyan gobe.

Albarkacin wannan rana ta bana BBC ta leka wani kauye da ke tsakiyar birnin Abuja da ake kira Gishirin Ruga, inda yaran makiyaya ke karatu.

Al'ummar sun shafe shekaru da dama suna rayuwa a kauyen amma basu da baben more rayuwa kamarsu makaranta da asibiti da sauransu.

Amma a baya-bayan nan wata mata ta ginawa kauyen makarantar firamare inda yaran makiyaya ke zuwa karatu. Makarantar mai aji daya ta kasance tana da malami daya.

Akasarin yaran da ke karatu a makarantar suna da burin zama likitoci da kuma malaman makaranta domin taimakawa al'ummarsu nan gaba.

Hajiya Maryam Abdulmumin Augie, ita ce matar da ta gina wannan makarantar domin taimakawa yaran su samu ilimi.