Arsenal na son Sesko, Guardiola ya kwaɗaitu da ɗan wasan Newcastle

SESKO

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta jero mutane 10 da take zawarcinsu a wannan kaka ciki harda ɗan wasan gaba a RB Leipzig daga Slovenian Benjamin Sesko, mai shekara 20 da mai taka leda a Sporting Lisbon Viktor Gyokeres, ɗan shekara 25, da kuma abokin da suke taka leda tare a Sweden, Alexander Isak, mai shekara 24. (Mirror)

Manchester United ta matsa kaimi kan ɗan wasan tsakiya a Everton, Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayinda suke son inganta bayansu a sabuwar kaka. (Telegraph)

Pep Guardiola ya kwaɗaitu da ɗan wasan Newcastle mai buga tsakiya Bruno Guimaraes, ɗan shekara 26, amma dole Manchester City ta kashe yuro mliyan 100 wajen saye shi. (Fichajes - in Spanish)

West Ham na sa rai Manchester City ta sake gabatar da tayi kan ɗan wasanta na Brazil da ke buga tsakiya, Lucas Paqueta mai shekara 26. (Football Insider)

Chelsea na cikin kungiyoyin da ke zawarcin mai tsaron ragar Athletico Paranaense, Bento ɗan shekara 24, wanda ya haska a fafatarwar Brazail da Ingila a makon da ya gabata. (Globo - in Portuguese)

Tottenham na son saye ɗan wasan Feyenoord da Mexico Santiago Gimenez, mai shekara 22, domin maye gurbin Harry Kane a wannan kaka - shekara guda bayan dan wasan mai shekara 30 daga Ingila ya koma Bayern Munich. (Caught Offside)

Ɗan wasan gaba a Liverpool Luis Diaz mai shekara 27, bai cire ran tafiya wata kungiyar Sifaniya domin buga La Liga ba a nan gaba a cewar mahaifinsa ɗan Colombia. (Daily Mail)

Manchester United na son saye ɗan wasan baya a Argentine, Aaron Anselmino mai shekara 18 daga Boca Juniors. (Ole - in Spanish)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kocin Brighton Roberto de Zerbi ya kasance wanda Bayern Munich ke son bai wa fifiko idan sun gaggara dauko tsohon ɗan wasan tsakiya Xabi Alonso daga Bayer Leverkusen. (Florian Plettenberg)

Tottenham da West Ham da Brighton da kuma Everton na shirya yadda kowanne su zai yi nasarar saye ɗan wasan Juventus da Ingila, Samuel Iling-Junior, mai shekara 20. (Football Insider)

Ɗan wasan tsakiya a Italiya Jorginho mai shekara 32, na iya bankwana da Arsenal a wannan kaka. (Football London)

Fatan Arsenal na saye ɗan wasan gefe Xavi Simons mai shekara 20 zai fuskanci kalubale saboda PSG na son ta cigaba da rike shi idan ya dawo daga zaman aro da yake yi yanzu haka a RB Leipzig. (Express)

Manchester United za ta amincewa ɗan wasan Denmark Christian Eriksen, mai shekara 32, ya tafi a karshen kaka. (Football Insider)

Ana yada jita-jita kan Real Madrid za ta saye ɗan wasan Liverpool da Ingila, Trent Alexander-Arnold, mai shekara 25. (Goal)

Ɗan wasan tsakiya a Jamus Toni Kroos, mai shekara 34, na shirin tsawaita zamansa da shekara guda a Real Madrid. (Fabrizio Romano)

Mai taimakawa kocin Liverpool Pep Lijnders na iya zama sabon kocin Ajax next a sabuwar kaka. (Telegraph - subscription required)