Hanyar magance tsangwama tsakanin ɗalibai a gargajiyance

Asalin hoton, Getty Images
Shahararrun mutane kamar Lady Gaga, Shawn Mendes, Blake Lively, Karen Elson, Eminem, Kate Middleton da Mike Nichols duk sun bayyana irin yadda aka dinga cin zalin su a makaranta da kuma ciwon da abin ya haifar masu a zuciya.
Wasu takwarorina, kamar Daniels daga ƙauyen Yorkshire na da ɗabi'ar kwaikwayon duk abin da na faɗa, saboda haka ba zan iya buɗe baki domin yin magana a cikin aji ba.
Tsawon shekaru cikin kunya
Duk yaron da aka zalunta zai fahimci girman matsalar kunya da irin wannan ɗabi'ar ke jaza wa mutum.
Kuma ba a nan matsalar ta tsaya ba. Bincike ya nuna cewa tasirin tsangwama ko zalunci da ake yi wa yara kan bi rayuwar mutum tsawon shekaru, abubuwan da ka iya shafar lafiyar ƙwaƙwalwarmu.

Asalin hoton, Getty Images
"A baya, mutane sun yi tsammanin halin tsangwama ba wani abin ƙyama ba ne, a wasu lokutan ma abu ne mai kyau - saboda yana taimaka wa rayuwar mutum," a cewar Louise Arseneault, farfesa a sashen ƙwaƙwalwa na Kwalejin King's da ke Landan.
"An ɗauki tsawon lokaci kafin masu bincike su gane cewa matsalar tsangwama abu ne da ke cutarwa."
Sakamakon wannan bincike, masu bincike da yawa na gwada hanyoyin yaƙi da ɗabi'ar.
Idan aka tsokani zuciya an tsokani jiki
Babu wata shakka cewa halin tsangwama na jefa yara cikin haɗari a lafiyarsu, inda aka nazarci cewa hakan ya haɗa da zaƙuwa, da damuwa da tunanin firgici.
Yayin da ake zaton damuwar za ta ƙare idan halayyar ta tsangwama ta tsaya, da yawa daga cikin waɗanda aka zalunta kan ci gaba da fuskantar matsalar ƙwaƙwalwa.

Asalin hoton, Getty Images
Lalurar firgici da son kashe kai
A cewar wata maƙala da aka wallafa a mujallar Harvard Review of Psychiatry, wata mace da aka tsangwama tana yarinya na fuskantar yiwuwar gamuwa da lalurar firgici sau 27 idan ta girma.
A cikin maza kuma, tsangwamar yara kan jawo yiwuwar tunanin kashe kai sau 18 da kuma aikata hakan.
Kazalika, tsangwama kan yi tasiri a hankalin mutum na tsawon lokaci a rayuwa; waɗanda aka zalunta kan fuskanci wahala wajen yin abokai a rayuwarsu, ballantana yin saurayi ko budurwa.
Fama kafin yarda da mutane
Akwai yiwuwar su yi fama wajen yarda da mutanen da suke rayuwa tare da su. "Yaran da aka tsangwama ka iya fassara abota ta hanya mai haɗari," a cewar Arseneault.
A ƙarshe kuma, akwai kuma matsalar ilimi da ta tattalin arziki. Tsangwama kan shafi ƙoƙarin ɗalibai, wanda kuma kan shafi yiwuwar samun aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Tsangwama game da luwaɗi da maɗigo
Ana iya yarda da wasu daga cikin tsangwamar da ake yi wa mutane saboda suna nuna irin bambancin da ake da shi a rayuwar al'umma.
Misali, yara da yawa da mahaifiyarsu ta zama 'yar maɗigo sun bayyana, a cikin wani bincike cewa ana tsangwamarsu saboda ɗabi'ar iyayensu.
Kazalika, matasan 'yan luwaɗi kan fuskanci tsangwama da sauran zalunci a makarantu fiye da saura. Sai dai makarantu kan kare yara daga irin nau'in na tsangwama.
Hanyar yaƙi da tsangwama a gargajiyance: Shirin Olweus
Cikin sa'a, ana sa ran bincike-binciken da ake gudanarwa a yanzu za su iya samar da hanyar yaƙi da ɗabi'ar tsangwama.
Shirin da ake kira Olweus Bullying Prevention Program na ɗaya daga cikin waɗanda aka jaraba. Wani marigayi ɗan Sweden, kuma ƙwararre kan ƙwaƙwalwa, Dan Olweus, shi ne ya ƙirƙire shi.
Kamar sauran hanyoyi, shirin na Olweus ya fara ne da gano matsalar. Saboda haka ne makarantu suka ƙirƙiri bincke ta hanyar tambayar ɗalibai game da halin da suke ciki.
"Sanin abin da yake faruwa a gidanku abu ne mai muhimmanci kuma zai taimaka wajen daƙile tsangwama," in ji Susa Lmber, wata farfesa kan ci gaban ƙwaƙwalwa a Jami'ar Clemson da South Carolina.

Asalin hoton, Getty Images
Ganawa tsakanin yara
A cikin azuzuwa, ɗaliban kansu kan shirya taruka domin tattauna matsalar tsangwama - da kuma hanyoyin da za su iya taimaka wa waɗanda ake tsangwama.
Ana yin hakan ne kawai domin a tabbatar cewa an raini al'adar yaƙi da matsalar a makarantu.

Asalin hoton, Getty Images
'Raguwar lamurra 2,000'
Ta hanyar aiki da Olweus, Limber ta gwada tsarin a wurare da yawa, ciki har da babban tsari kan makarantu fiye da 200 a Pennsylvania.
Bincikensu ya ce an samu raguwar tsangwama sau 2,000 cikin shekara biyu. Haka nan, an ga sauyawar halin ɗalibai game da tsangwama.
Ba binciken Lmber ne kaɗai ya nuna cewa jajircewa wajen wayar da kai za ta sauya lamarin ba.

Asalin hoton, Getty Images
Kyautatawa kulawa ce
Ba a makaranta kawai tsangwama ta tsaya ba, kuma Limber ta gargaɗi iyaye da masu kula da yara cewa su dinga lura da matsalar.
"Ya kamata a mayar da hankali kan magana a kan halayyar nan - kar a jira sai lamarin ya faru," a cewarta.
Ta jaddada cewa lallai manya su damu da damuwar yara - ko da kuwa ana kallon lamuran ƙanana.

Asalin hoton, Getty Images
David Robson marubuci ne a Landan.











