Auren zawarawa a Kano da motocin agaji zuwa Gaza cikin hotunan Afirka

An wallafa

Wasu ƙayatattun hotunan Afirka da na 'yan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata

.

Asalin hoton, KOLA SULAIMON/AFP

Bayanan hoto, A makon da ya gabata ne aka yi shagalin bikin auren zawarawa da 'yan mata 1,800 a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
.

Asalin hoton, ADEKUNLE AJAYI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, An gudanar da walima a wani ɓangare na shagalin bikin a birnin Kano.
.

Asalin hoton, ADEKUNLE AJAYI/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Jama'a da dama sun taru bikin Ranar Motsa Jiki ta 'Arise Walk for Life' a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yan sanda sun harba wa dandazon masu zanga-zanga hayaƙi mai sa hawaye a babban birnin ƙasar Mozambique ranar Talata.
.

Asalin hoton, FRANCK FIFE / AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan zari ruga daga ƙasar Afirka ta Kudu Kurt-Lee Arendse yayin karawar kusa da ƙarshe da Faransa a ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, AARON UFUMELI/EPA

Bayanan hoto, An gudanar da gasar sarauniyar kyau tsakanin Zabaya a Zimbabwe karon farko a duniya, da nufin kawo ƙarshen tsangwamar masu fama da lalurar.
.

Asalin hoton, JEFF SCHEAR/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Dafa-dukan shinkafa samfurin ƙasar Laberiya na ɗaya daga cikin abincin da aka baje kolinsu a birnin New York na Amurka ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, LEGNAN KOULA/EPA

Bayanan hoto, An girbe cocoa a Adzopé da ke ƙasar Ivory Coast, bayan dakatar da hada-hadar cocoa a yankin saboda ruwan sama mai karfi.
.

Asalin hoton, AMOS GUMULIRA/AFP

Bayanan hoto, Ranar Lahadi ƴan rawar Gulewamkulu na cashewa a lokacin bikin ranar al'adun gargajiya da gidauniyar Chewa Heritage ta shirya a Lilongwe da ke ƙasar Malawi.
.

Asalin hoton, EMMANUEL CROSET/AFP

Bayanan hoto, A Afirka ta Kudu Jami'an lafiya sun bayar da magani kyauta ga marasa lafiya da suke rayuwa a ƙauyuka
.

Asalin hoton, KHALED DESOUKI/AFP

Bayanan hoto, Hoton shugaban ƙasar Masar a jikin motoci ɗauke da kayan abinci da zuwa Gaza a ranar Litinin