Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bai wa Lewandowski jan kati karo na biyu a tarihi
An bai wa Robert Lewandowski jan kati karo na biyu a tarihin sana'ar kwallon kafa a gidan Osasuna ranar Talata a gasar La Liga.
Barcelona ce ta yi nasara da ci 2-1 a gidan Osasuna a wasan mako na 14 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya wasannin mako na 14.
Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki biyar tsakaninta da Real Marid ta biyu.
David Garcia ne ya fara ci wa Osasuna kwallo minti shida da take leda, sai dai Barcelona ta farke ta hannun Pedro Gonzalez Lopez, bayan da suka koma daga hutu.
Sauran minti biyar a tashi daga wasan kungiyar Nou Camp ta kara na biyu ta hannun Raphinha ta hada maki ukun da take bukata.
To sai dai tun a minti na 31 alkalin wasa Gil Manzano ya bai wa Robert Lewandowski jan kati, sakamakon gula da ya yiwa David Garcia.
Tun farko an bai wa tsohon dan kwallon Bayern Munich katin gargadi kan rike Nacho Vidal da ya yi a minti na 11 da fara wasa.
Daga baya aka kara masa kati mai ruwan dorawa, sannan aka daga masa jan katin da mai buga tamaula baya kauna.
Wannan shi ne karo na biyu da aka bai wa Lewandoski jan kati, kenan ba zai yi wa Barcelona wasan da za ta buga da Espanyol ba a La Liga, bayan kammala gasar kofin duniya.
Za a fara gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Jan katin da aka fara bai wa Lewandowski shi ne a lokacin da yake taka leda a Borussia Dortmund a 2013.