An bai wa Ronaldo fenariti amma ya bukaci rafli ya soke hukuncin

An wallafa

Cristiano Ronaldo ya yi kaurin suna a cin kwallaye, sai dai ranar Litinin dan wasan Al-Nassr ya bukaci alkalin wasa ya soke fenaritin da ya busa.

Mai shekara 38 ya fadi a gurbin bayar da fenariti a minti na biyu da taka leda. bayan da aka yi masa keta a wasa da Persepolis.

Al-Nassr na buga gasar zakarun Asia da kungiya daga Iran.

Bayan da alkalin wasan dan kasar China, Ma Ning ya hura bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai Ronaldo ya bukaci a soke hukuncin da cewar ba fenariti bane.

Hakan ya sa alkalin wasa, Ming ya je ya duba na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci daga nan aka soke fenaritin.

Bayan da alkalin wasa ya je ya kalli abinda ya faru a VAR da kuma gaskiyar da Ronaldo ya tsaya cewar ba fenariti bane, hakan ya hana a fara cin Persepolis.