Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da za a rika tunawa game da shugaban Kenya mai barin gado Uhuru Kenyatta
Wata rana a shekarar 2018 wani dalibi ya tambayi shugaban Kenya Uhuru Kenyatta a kan da me za a rinka tunawa da shi idan ya bar mulki? Sai ya yi shiru saboda tambayar ta zo masa da ba-zata.
Daga nan sai ya ce, “Na farko zan bar kasa dunkulalliya, kuma mai cike da al’ummar da ke da hadin kai. Na biyu shi ne mun yi nasarar yaki da cin hanci.”
A yayin da yake shirin sauka daga mulki ya mika wa tsohon abokinsa wanda daga baya ya zama abokin adawarsa, William Ruto, shi za a iya cewa ya cimma wadannan nasororin da ma wasu?
Abu mafi muhimmanci da ya yi wajen hada kan kasar shi ne a watan Maris din 2018, lokacin da suka sha hannu tare da jagoran ‘yan adawa kuma tsohon firaiminista Raila Odinga, a matsayin wata alama ta kulla alakar siyasa.
An samu fahimtar juna ta tsawon watanni bayan tarzomar da ta biyo bayan soke zaben da aka yi a 2017 da Kotun Kolin kasar ta yi da kuma matakin kaurace wa zaben da aka sake yi da Mr Odinga ya yi, inda daga bisani ya shirya bikin rantsar da kansa a Nairobi babban birnin kasar.
To amma yarjejeniyar da Uhuru Kenyatta da Raila Odinga suka kulla ba ta samu karbuwa ba a wajen mataimakin shugaban kasa William Ruto, wanda ya ce yarjejeniyar ta rusa kudurinsu na bunkasa samar da abinci da harkar lafiya da samar da gidaje masu rahusa da kuma bunkasa bangaren masana’antu a kasar.
Wannan dalili ne ya sa da sannu a hankali dangantaka ta fara tsami tsakaninsa da Mr Kenyatta, wanda a hankali ya janye goyon bayan da yake bai wa Mr Ruto, ya kuma koma goyon bayan abokin adawarsa Mr Odinga a zaben kasar da aka yi a watan Agusta.
An ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin Kenyatta da mataimakinsa har zuwa bayan zabe.
Har kawo yanzu kuma bai fito fili ya ta ya shi murnar samun nasara a zaben da aka yi ba.
Hadin kan da Mr Kenyatta ya yi fatan tabbatarwa bai yiwu ba, to amma masu sharhi sun ce yana da matukar muhimmanci ga kasar ta guji fadawa cikin rikicin kabilanci wanda ta fuskanta bayan zaben 2007, a inda mutum 1,200 suka mutu dubbai kuma aka tilasta musu barin muhallansu.
Bisa la’akari da yadda aka gudanar da zaben da ya gabata cikin lumana, masu sharhi sun ce ko shakka babu Mr Kenyatta ya cimma burinsa na hada kan kasa da kuma samar da al’umma mai hadin kai duk da mutumin da yake goya wa baya Mr Odinga ya fadi zabe.
Rashin fitaccen dan adawa da zai rinka sanya idanu a kan lamuran gwamnati ya taimaka wajen gazawar gwamnatin Mr Kenyatta na kawo karshen cin hanci da kuma magance barnatar da kudaden al'umma.
Wani kwararre ya ce kasar na asarar kusan shili biliyan biyu a kowacce rana kwatankwacin dala miliyan 17 a kan cin hanci.
Gwamnatin Mr Kenyatta, ta zuba jari sosai a wajen masar da ababen more rayuwa a sassan kasar, ciki har da bayar da aikin manya-manyan kogunan kasar da gina filayen wasanni da samar da hasken lantarki da inganta ayyukan jiragen kasa musamman wajen gina babban layin dogo a Nairobi.
An gudanar da wadannan ayyuka ne ta hanyar ciwo bashi.
Abin tambayar shi ne shin ko an aiwatar da ayyukan da aka ciwo bashin don su?
Misali, layin dogon da wani kamfani China ya gina wadda ta taso daga Mombasa zuwa Nairobi, an kashe dala biliyan uku da miliyan dari biyu, abin da masu sharhi suka ce kudin ya yi yawa, idan aka kwatanta da abin da kasashe makwabtan Kenya kamar Tanzani da Ethiopia suka kashe a irin wannan aikin.
Bashin da aka ciwo ya sa kasar ta fada matsalar kangin bashi wadda za ta kwashe shekara da shekaru tana biya.
A karshen 2021, bashin da ake bin kasar ya kai dala biliyan $72, abin da ke nufin ya kai kashi 68 cikin 100 na kudaden da kasar ke samu, idan aka kwatanta da kashi 38 na kudaden da ake samu kafin Mr Kenyatta ya zama shugaban kasa a 2013.
Yayin da masu sanya idanu ke cewa kasar na bukatar sabbin ababen more rayuwa don bunkasa tattalin arzikin kasar da ke gabashin Afirka, sun bayyana damuwa a kan yadda za a yi facaka da kudade.
Mr Hira ya ce ba matsalace a ranto kudi ba, batun shi ne ta yaya za a yi amfani da shi?
A shekarar 2013, Mr Kenyatta ya yi alkawarin saya wa yara ‘yan makaranta komfutocin hannu don taimaka musu samun ilimin fasahar intanet da ta zamani.
To amma hakan bai yiwu ba, saboda wasu kayan da aka kai wasu makarantun an bar su ba a amfani da su har aka sace wasu.
Duk da sukar da ake yi wa gwamnatin Kenyatta a kan tabarbarewar ilimi, masu sanya idanu sun ce an samu sauye-sauye don an kawo canji a tsarin ilimin kasar.
Haka kuma a bangaren lafiya, gwamnatin ta sa ta yi rawar gani wajen samar da wasu abubuwan kamar gina sabbin asibitoci da samar da kuma karin gidajen kwanciyar marasa lafiya a asibitocin gwamnati.
Idan aka auna a mizani, za a iya cewa an samu ci gaba da sauye-sauye a Kenya a cikin shekaru 10.
A takaice dai, baya ga sauyi, Kenya ta fuskanci kalubale na ba-zata a lokacin mulkin Kenyatta, kamar hare-haren masu ikirarin jihadi a Nairobi da kuma wasu wurare da annobar korona da kuma tashin farashin kayayyaki wanda yakin Rasha da Ukraine ya haddasa.
A yayin da Mr Kenyatta zai mika ragamar mulkin kasar ga wanda zai gaje shi, kalubalen da ke gaban gwamnati mai zuwa shi ne na yadda za ta cika alkawuran da ta dauka da kuma yadda za ta yi abubuwan da ‘yan kasar ke bukata kamar samar da aikin yi da magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki.