Yadda ƴan siyasa ke wankin banɗaki da yankan kayan miya don jan hankalin masu zabe a Kenya

An wallafa

Wasu 'yan siyasar Kenya sun jingine rayuwarsu ta jin daɗi zuwa wankin banɗaki, da tsinkar kayan marmari, da dafa shayi a yunƙurinsu na jawo hankalin masu jefa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar da za a yi ranar 6 ga watan Agusta.

Ɗaya daga cikin mutanen da ya fi nishaɗntar da 'yan Kenya shi ne Polycarp Igathe, wanda ya saka takalmi har ƙwauri da kuma safar hannu kafin daga bisani ya ɗauki abin shara da botiki yana wanke banɗakin jama'a a Nairobi babban birnin ƙasar.

Ya shafe kusan daƙiƙa 20 yana wanke banɗakin, yayin da ma'aikata suka saki baki suna kallon sa.

"An daɗe ana kallon wannan abin a matsayin aikin datti amma wannan aiki ne muhimmi," a cewar Mista Igathe.

Kazalika, Mista Igathe da ke neman zama gwamna Nairobi, an gan shi yana wanke motoci da kuma zuba wa mutane giya a wani gidan yawon dare.

Mutane sun yi tsokanar sa da cewa ya kamata ya fara rainon yara da sauran ayyukan gida.

Igathe ne mataimakin gwamna ƙarƙashin Mike Sonko, amma ya sauka daga muƙaminsa ƙasa da shekara ɗaya yana mai cewa sun kasa daidaitawa da gwamnan.

Masu sharhi kan lamuran siyasa na cewa masu zaɓe sun saba da irin wannan kamfe ɗin na neman ƙuri'a kuma ba lallai hakan ya yi tasiri ba.

Johnson Sakaja, wanda sanata ne, shi ne babban mai hamayya da Igathe.

Shi ma ba baƙon irin wannan abubuwa ba ne, inda ya sha wallafa hotunansa yana sayen kifi a gefen titi, da sayen kayan miya a kasuwa ba a manyan kantunan ƙasar ba.

Mista Sakaja ya kasance sanata mai wakiltar Nairobi tun 2017 kuma wannan ne karon farko da zai yi takarar gwamna.

Wata mazauniyar Nairobi, Anne Wambui, ta nuna damuwar cewa 'yan siyasa ba su san ma inda kasuwanni suke ba sai zaɓe ya zo.

"Muna ta faman yadda za mu tsira da rayuwarmu a wannan birnin amma idan zaɓe ya zo sai wani ya zo ya nuna mana ya san halin da muke ciki saboda yana son ƙuri'unmu," kamar yadda ta faɗa wa BBC.

Shi kuma ɗan majalisa daga Kimilili mai suna Didmus Barasa, yakan yi nasa kamfe ɗin ta hanyar hawa acaɓa ko okada maimakon motocinsa masu tsada.

Yakan shiga cikin baro da aka ɗora a kan motarsa. Ya mayar da baron wata alamar kamfe ɗinsa da yake amfani da shi wajen neman ƙuri'ar matasan Kenya.

Haka nan, an ga Mista Barasa na shan shayi tare da mutanen gari a wani otel. A wani hoton, an gan shi yana dafa shayin a kan murhun gargajiya mai dutse uku ga wata dattijuwa mai shekara 67 sanye da takalmansa masu tsada.

Sai dai kuma bai yi nasarar samun goyon bayan kowa da kowa ba da wannan ƙoƙari nasa, inda yake yawan samun martani marasa daɗin ji a shafukan zumunta.

Tsohon ɗan majalisar Kakamega, Boni Khalwale wanda ya sake tsayawa takara, ya zaɓi ya nuna tasa dabarar ce ta hanyar wanke takalminsa a gefen titi.

Ya zauna yana cin masara tare da mutane kafin a gama wanke masa takalman.

Ɗan majalisar Embakasi ta Yamma mai suna George Theuri ya wallafa hotunansa yana tafiya ba takalmi a kan titi kuma ya ce: "Ina jin daɗin lokacina a unguwarmu."

Mista Theuri na sanye da gajeren wando a lokacin, abind a ya sa wani ya yi martani a shafukan zumunta da cewa "sai mutum ya cika cikakken jahili zai yarda da 'yan siyasar nan".

Wata biyar da suka wuce Sanata Isaac Mwaura ya yi duk mai yiwuwa don ya samu tikitin takarar ɗan majalisa a Nairobi ta hanyar taimaka wa 'yan kasuwa gyara kayan miya.

Mista Mwaura ya ce yana ƙoƙarin fahimtar irin gwagwarmayar da masu ƙananan sana'o'i ke yi ne a mazaɓarsa ta Ruiru da ke Nairobi.

"Abin baƙin ciki...ba ku taɓa sanin rayuwar mama da baba mboga ba [masu sayar da kayan miya] sai yanzu. Har sai da shekarar zaɓe ta zo sannan muka fahimci hakan," a cewar wani ma'abocin shafukan zumunta.

Dukkan alamu sun nuna kamfe ɗin bai amfane shi ba, saboda bai samu tikitin takarar ba kuma babu shi za a fafata a zaɓen na ranar Talata mai zuwa.