Me ke haifar da tsaiko a naɗin Jakadun Najeriya zuwa ketare?

An wallafa

Wasu 'yan Najeriya sun soma nuna damuwa kan dogon lokacin da gwamnatin kasar ta dauka, ba tare da tura jakadunta wasu kasashen ketare ba.

Masu nuna damuwa na baya-bayan nan, su ne masana diflomasiya, inda suka ce bai kamata kasa kamar Najeriya ta yi jinkirin irin haka ba.

To sai dai masana difomasiya kamar Ambasada Sulaiman Dahiru tsohon jakadan Najeriya a Sudan, ya ce rashin tura wakilan ya nuna cewa gwamnatin kasar ba ta dauki harkar alakarta da sauran kasashen waje da muhimanci ba.

''Gwamnati ta yi kuskure, bai kamata su yi wa jakadunsu da ke kasashen waje kiranyen su dawo gida ba alhalin ba su shirya wadanda za su maye gurbinsu ba.

"A tsari bai kamata Jakada ya bar kasa har na sama da mako biyu ba tare da an tura wanda zai maye gurbin shi ba.

Wannan zai sanya kasashen su yi tunanin ba a daukji mu'amala da su da muhimmanci ba.

Tun watan 9 na bara aka yi wa Jakadun Najeriya kiranye, hakan na nufin duk abin da Najeriya ta ke son bibiya ba za ta yi ba saboda ba ta da wakili,'' in ji Ambasada Dahiru.

Ya kara da cewa a baya-bayan nan an ce an kai sunayen wadanda ake ganin za a tura kasashen, hakan na nufin tuntuni ba a yi wannan tanadi ba.

''Ina ganin abin da ke kawo jinkirin a ganina an sanya siyasa, saboda ana debo 'yan siyasa a cusa a aikin diflomasiya alhalin ba su da kwarewa a wannan fannin, dan haka gwamnati ta yi kokarin ganin Najeriya ta samu wakilci a kasashen da ba ta da jakadu.''

A watan Oktobar bara ne dai shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jakadun kasar da ke kasashen ketare kiranye, a lokacin an yi tunanin cikin takaitaccen lokaci za a nada wadanda za su maye gurbinsu.

Sai dai har yanzu hakan ba ta samu ba.

Rashin tura wadannan jakadu abu ne da ake ganin zai iya tasiri a harkokin diflomasiya tsakanin Najereriya da kasashen ketare.

Gwamnati dai babu wani sanarwa ko cikakken bayanai da ta fitar kan jinkirin. Ana dai cigaba da zuba ido domin ganin tsawon lokacin da za a dauka wajen tura sabbin jakadun.