Najeriya ta yi martani kan harin da aka kai wa 'yan ƙasarta a Jami'ar Indiya

An wallafa

Gwamnatin Najeriya ta ce ta samu rubutaccen tabbaci daga Hukumomin Indiya cewa za su kare ɗalibanta da ke can.

Shugabar Hukumar kula da harkokin 'Yan Najeriya Mazauna Ƙetare, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana haka lokacin da take mai da martani ga rahotannin cewa an kai wa 'yan Najeriya hari a wata jami'ar ƙasar Indiya.

A ranar Litinin ne, wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna yadda rigima ta kaure a wata harabar jami'ar da ke birnin Delhi.

Wani Farfesa a fannin binciken rikice-rikice da zaman lafiya, Ashok Swain ne yaɗa bidiyon rigimar a dandalin tiwita inda ya rubuta cewa;"Ana far wa ɗaliban Najeriya da suka zo karatu ƙasar Indiya a harabar wata Jami'a da ke kusa da birnin Delhi - ɗaliban Najeriya 30,000 ne suka biya kuɗi don yi karatu a Indiya, yayin da 'yan Indiya 50,000 ke zaune a Najeriya suna neman kuɗi. "

An yi ta tura saƙon Farfesa Ashok tare da mai da martani a shafukan sada zumunta har ya kai ga Abike Dabiri-Erewa ta zo ta yi bayani game da haƙiƙanin abin da ya faru.

Kafofin yaɗa labarai na ƙasar kamar The Times of India na bayyana Jami'ar GD Goenka ta Gurugum a matsayin inda rigimar ta tashi.

Jaridar ta ruwaito cewa ɗaliban Najeriya 60 daga Jami'ar GD Goenka ne suka tsere daga harabarta bayan wani ya yi zargin an doke shi tare da ci masa zarafi a filin ƙwallon ƙafa da kuma a ɗakunan kwanansu.

A cewar Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar kula da harkokin 'yan Najeriya mazauna ƙetare, lamarin ya faru ne ranar Asabar.

Ta ce lamarin ya auku ne sanadin wata rigima da ta tashi a lokacin wani wasan ƙwallon ƙafa tsakanin ɗaliban Afirka da na Indiya.

Abike ta ce ɗaliban Afirka da na Indiya sun kara ne a wata gasar ƙwallon ƙafa wadda daga bisani ta koma tashin hankali, har ta kai 'yan Indiya suna yi wa 'yan Afirka barazana.

Ta ce ofishin jakadancin Najeriya a Indiya cikin gaggawa ya kai ɗauki inda ya bai wa ɗaliban jami'ar 86 mafaka, kuma suka kwana a ofishin har zuwa washe gari ranar Lahadi.

Ofishin jakadancin Najeriyar ya kuma gayyaci wakilan gwamnatin Indiya inda suka ba shi tabbaci game da tsaron lafiyar ɗaliban Najeriya.

Abike ta ce tuni ɗaliban Najeriya suka koma jami'arsu ranar Lahadi kuma a ko'ina suna cikin kwanciyar hankali.

Ta ƙara da cewa an ba da rahoton cewa mutane ƙalilan sun ji raunuka, amma dai ana gudanar da bincike.

"Ma'aikatar harkokin ƙasashen wajen Indiya ta bayyana ƙarara cewa su ne da alhaki matuƙar wani abu ya sake faruwa ga ɗaliban Najeriya," in ji Abike.

Ta ce tuni hukumomin Indiya suka bai wa Najeriya tabbaci a rubuce don kare ɗaliban ƙasarta. “Duk ɗalibin da aka yi wa barazana, ya garzaya ya kai rahoto ga ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin Delhi cikin gaggawa.”

A lokaci guda kuma, hukumomin Jami'ar GD Goenka sun ƙi cewa uffan game da wannan lamari da ya faru.

BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar jami'ar ta hanyar imel da lambar waya amma babu amsa har lokacin haɗa wannan rahoto.

Hari kan ɗan Najeriya ko 'yan Najeriya a ƙasar Indiya ba sabon abu ba ne.

A shekara ta 2017 ma, an samu rahotannin cewa wasu 'yan ta-more sun far wa wasu ɗaliban Najeriya a yankunan da ke wajen Delhi, babban birnin ƙasar.