Arsenal ta koma ta daya a teburin Premier League

An wallafa

Arsenal ta koma ta daya a teburin Premier League, bayan da ta yi nasara 2-0 a kan Wolverhampton a Molineux ranar Asabar.

Gunners ta ci kwallon da ya sa ta dare kan teburin ta hannun Leandro Trossard a minti na 45, sannan Martin Odegaard ya kara na biyu daf da za a tashi.

Hakan ya sa Gunners tana ta daya da maki 74, bayan wasan mako na 34, yayin da Liverpool mai maki 71 ta biyun teburin za ta fafata da Fulham a Craven Cottage ranar Lahadi.

Ranar Asabar Manchester City ta kai wasan karshe a FA Cup, bayan da ta yi nasara a kan Chelsea 1-0 a Wembley.

Arsenal ta kafa tarihin yin wasa shida a jere a waje a lik ba tare da kwallo ya shiga ragar ta ba, tun bayan bajintar Liverpool a kakar 2014/15.

Wasa na shida a jere kenan da Gunners ta yi nasara a kan Wolverhampton, wadda ta doke 2-1 a wasan farko a Emirates ranar Asabar 2 ga watan Satumba.

Karo na biyu kenan da Wolves ta kasa zura kwallo a raga a gida a wasa 27 tun bayan Fabrairu da Brentford ta zura mata 2-0 a Molineux.

Kofi daya ne ke gaban Arsenal da take fatan dauka, shi ne Premier League, bayan da Bayern Munich ta yi waje da ita a Champions League ranar Laraba a Jamus.

Tun farko sun tashi 2-2 a Emirates a makon jiya a gasar Zakaraun Turai, sai Bayern ta ci 1-0 a zagaye na biyu a Jamus.