Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona da Man City na gogayya kan Olmo, Ƙila Marquez ya maye gurbin Xavi
Barcelona da Manchester City sun tattauna da wakilan dan wasan tsakiya na RB Leipzig Dani Olmo na Sifaniya, mai shekara 25 a makon da ya gabata. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Chelsea da Barcelona na daga cikin kungiyoyin Turai da yawa da suke son sayen dan wasan Roma, Paulo Dybala, na Argentina. (Rudy Galetti)
Tsohon dan bayan Mexico Rafa Marquez na daya daga cikin wadanda ake ganin za su maye gurbin Xavi, idan kociyan dan Sifaniya ya bar Barcelona a karshen kaka. (ESPN)
Bayern Munich da Tottenham sun bi sahun Manchester United wajen neman matashin dan bayan Everton Jarrad Branthwaite na Ingila. (Teamtalk)
Kungiyoyin Saudiyya na son dan wasan tsakiya na Senegal Idrissa Gana Gueye, mai shekara 34, wanda ba lalle ba ne Everton ta sabunta kwantiraginsa idan ya kare a karshen kaka. (Football Insider)
Newcastle da Liverpool sun shiga gogayyar zawarcin dan bayan Sporting Lisbon Ousmane Diomande mai shekara 20, na Ivory Coast, wanda Chelsea ma ke so.(Football Transfers)
Newcastle ta tura masu nemo mata 'yanwasa, domin duba matashin dan wasan tsakiya na Boca Juniors' Kevin Zenon mai shekara 22, dan Argentina da kuma, dan baya, Nicolas Valentini mai shekara 23, shi ma dan Argentina. (HITC)
Kociyan Everton Sean Dyche ba ya fuskantar hadarin rasa aikinsa duk da rashin katabus da kungiyar ke yi. (i news)
Nottingham Forest na son sama da fam miliyan 20 a kan dan bayanta Murillo, dan Brazil mai shekara 21, yayin da Liverpool, da Chelsea, da Manchester United, da kuma Paris St-Germain ke sonshi. (Football Insider)
Watakila Manchester United ta bayar da Mason Greenwood a cinikin da za ta yi na sayen dan bayan Juventus Gleison Bremer, na Brazil, mai shekara 27. (Gazzetta dello Sport)