Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An bukaci Juventus ta biya Ronaldo £8.3m
Wata kotu a Italiya ta umarci Juventus ta biya Cristiano Ronaldo albashin £8.3m.
Ronaldo mai shekara 39, ya amince a jingine albashinsa a lokacin da aka samu tsaikon cutar korona a kakar 2020-21.
Dan kasar Portugal ya ce yana bin sama da £17m da ya kamata a biya shi.
Kotun ta ce ya kamata dan wasan ya karbi albashinsa, bayan an cire haraji da wasu kudin ka'ida.
Ronaldo ya yi kaka uku a Italiya a Juventus tsakanin 2018 zuwa 2021, wanda ya taimaka ta dauki kofin Serie A biyu.
Daga nan ya koma Manchester United, wadda ya yi wata 16 a Old Traffordsai ya koma Al-Nassr ta Saudi Arabia.
Zakaran Ballon d'Or karo biyar - shi ne kan gaba a matakin dan wasan da yafi karbar albashi a 2023 da yake karbar £109m in ji Forbes.