Mutum biyu sun mutu a harin da ɗaliba ta kai makarantarsu a Amurka

'Yansandan Amurka da sauran jami'an tsaro

Asalin hoton, OTHERS

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

'Yansanda a jihar Wisconsin ta Amurka sun ce wata budurwa 'yar shekara 15 ce ta kai harin bindiga da aka kai kan wata makaranta a ranar Litinin.

Mutane biyu aka kashe a harin sannan ita ma 'yar bindigar ta mutu.

Akwai kuma mutane shida da suka jikkata, biyu daga cikinsu na mawuyacin hali.

Ta'adar bude wuta a kan jama'a masu yawa ko harbin kan mai uwa da wabi a Amurka ba wani sabon abu ba ne, to amma abin da yake ba a saba gani ba sosai shi ne a ce mace ce ta kai irin wannan hari.

A yanzu dai kwararrun masu bincike na can sun dukufa domin gano ainahin abin da ya angiza wannan budurwa mai shekara 15 Natalie Rupnow, ta bude wuta a kan 'yan ajinsu, a wannan makaranta ta 'yan Mishan - 'Abundant Life' da ke birnin Madison na jihar ta Winsconsin

A harin mutum biyu malami ko malama da dalibi ko daliba sun rasu, mutum shida sun ji rauni - biyu daga cikinsu raunin ya yi tsanani, kafin ita ma dalibar ta juya bindigar ta hallaka kanta da kanta.

Wannan shi ne yadda ake ta samun karuwar harin bindiga a makarantu, abin da ya kai ga wani ayarin ma'aikatan lafiya ke ta samun horo da gwaji a wata cibiya a kusa da inda aka kai harin, yadda za su fuskanci irin wannan hari a duk lokacin da aka kai shi.

jami'ai sun ce sun samu kiran bukatar agajin gaggawa ne kan harin daga wani dalibi dan shekara bakwai ko takwas.

Shugaban Amurkar Joe Biden ya kara kira ga majalisar dokokin kasar da ta tsaurara matakan mallakar bindiga, duk da cewa 'yan majalisar sun kawar da kai daga irin wannan kira da ya sha yi a baya a kasar da 'yancin mallakar bindiga ke cikin tsarin mulkinta.