Gane Mini Hanya: Tare da tsohon ƙaramin ministan gidaje 09/11/2024
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
A karon farko tun bayan sauke su daga muƙaman ministocin Najeriya, tsohon ƙaramin ministan gidaje, Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ya ɓara.
Matakin dai ya zo wa ƴan Nijeriya masu yawa, da ba-zata, ganin irin kusancinsa a siyasance da Shugaba Bola Tinubu.
Shi dai shugaban na Najeriya tun da farko ya yi alƙawarin cewa zai sauke ministocinsa da ba su yi wani ƙoƙarin a-zo-a-gani ba a muƙaman da ya ba su amana.









