Chelsea ta yi wa Aston Villa tayin Sterling, Ayew zai koma Leicester

Raheem Sterling

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea ta yi wa Aston Villa tayin ɗanwasanta na gaba mai shekara 29 Raheem Sterling, amma Unai Emery ba ya da tabbacin ko ɗanwasan na Ingila zai dace da tsarinsa. (Mirror)

Sterling dai ba ya da tabbas kan makomarsa a Chelsea kuma ba ya son zuwa Saudiyya. (Mail)

Leicester City na dab da ɗaukar ɗanwasan gaba na Crystal Palace da Ghana mai shekara 32 Jordan Ayew. (Sky Sports)

Kocin ƙungiyar Leicester Steve Cooper na kuma lissafin ɗauko ƴanwasan tsakiya biyu kafin rufe kasuwar ƴanwasa. (Telegraph - subscription required)

Norwich City na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗauko ɗanwasan Brazil mai shekara 22 Reinier daga Real Madrid. (O Globo - in Portuguese)

Tottenham na shirin ba Stoke aron matashin ɗanwasan baya Ashley Phillips mai shekara 19. (Athletic - subscription required)

Girona ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 21.2 da Watford kan ɗanwasan tsakiya na Colombia Yaser Asprilla, mai shekara 20. (Sky Sports)

Brighton da Real Sociedad da Real Mallorca na ribibin ɗanwasan baya na Jamus Mats Hummels mai shekara 35. (Florian Plettenberg)

Barcelona ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 11 kan ɗanwasan gaba na Italiya Federico Chiesa, mai shekara 26, daga Juventus. (Sport - in Spanish)

Everton da AC Milan da Bayern Munich da wasu ƙungiyoyin Turkiya na hamayya kan ɗanwasan baya na Newcastle da Ingila Kieran Trippier, mai shekara 33. (Talksport)

Brentford na dab da kammala cinikin ɗanwasan Brazil mai shekara 18 Gustavo Nunes daga Gremio. (Fabrizio Romano)

Ɗanwasan baya na Jamhuriyyar Ireland John Egan, mai shekara 31 na atisaye da Burnley bayan ya bar Sheffield United. (Football Insider)