Tonali na daf da fara taka leda a Newcastle

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle United ta ce Sandro Tonali zai fara buga wasa daga ranar 28 ga watan Augusta bayan an dakatar da shi na wata 10 sakamakon saɓa dokokin caca.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Italiya (FIGC) ta hukunta ɗan wasan mai shekara 24 a watan Oktoban da ya gabata bayan ya keta dokar da ta hana ƴan wasa yin caca kan wasannin ƙwallon ƙafa da hukumar ko UEFA ko kuma FIFA suka shirya.
Dan wasan na Italiya ya koma Newcastle ne daga AC Milan a watan yulin 2923 kan farashin fam Miliyan 55 kuma an dakatar da shi ne bayan ya bugawa ƙungiyar wasanni 12.
Wasan farko da Tonali zai buga na iya kasancewa a gasar cin kofin Carabao da Nottingham Forest amma hakan ya danganta kan lokacin da za a buga a makon da zai dawo taka leda.
Tonali ya na atisaye da tawagar Newcastle gabannin fara gasar Firimiyar bana.
A ranar Juma'a 16 ga watan Agusta ne za a fara gasar ta bana, yayin da wasan farko na Newcastle zai kasance a gida da Southampton a ranar Asabar, 17 ga watan Augusta.






