Ƴan Barcelona 10 ne za su buga wa tawagoginsu tamaula

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan wasan Barcelona 10 aka gayyata, domin buga wa tawagoginsu wasanni, bayan da aka ware wannan makon don buga fafatawar.
An buga wasa huɗu a La Liga kawo yanzu, an kuma kira ƴan Barcelona bakwai da zasu buga wa kasashensu Nations League a cikin Satumba.
Sauran ƴan wasa uku za su kara a wasan matasa ƴan kasa da shekara 21 da kuma karawar sada zumunta.
Waɗanda aka gayyata buga Nations League
Ranar Juma'a 30 ga watan Agusta, kociyan Sifaniya, Luis de la Fuente ya gayyaci ƴan wasan da za su buga wa kasar Nations League, ciki har da Dani Olmo da Ferran Torres da Pedri da kuma Lamine Yamal.
Sifaniya, mai rike da Euro 2024 za ta kara da Belgrade ranar Alhamis 5 ga watan Satumba, sannan ta kece raini da Switzerland a Geneva kwana uku tsakani.
Shi kuwa Jules Kounde zai buga wa Faransa Nations League da za ta fafata da Italiya da Belgium, yayin da mai tsaron raga, Ter Stegen zai yi wasan da Jamus za ta kara da Hungary da kuma Netherlands.
Daga karshe Robert Lewandowski zai buga wa Poland Nations League da za ta yi da Scotland da kuma Croatia.
Waɗanda aka gayyata karawar ƴan kasa da shekara 2i da wasan sada zumunta
Shi kuwa Pablo Torre da kuma Cubarsí an gayyace su cikin tawagar matasan Sifaniya ƴan kasa da shekara 21.
Za su maye gurbin Fermín López da Santi Denia, waɗanda ke jinya.
An kuma kira Diego Kochen tawagar Amurka, domin buga wasan sada zumunta da Canada da kuma New Zealand.
Barcelona tana mataki na ɗaya a kan teburin La Liga da maki 12, bayan lashe wasa huɗu da fara kakar nan, ita kaɗai ce ta lashe dukkan karawa huɗu.









