Liverpool ta miƙa wa Alexander-Arnold kwantiragin £78m, Napoli na son Chiesa

Trent Alexander-Arnold

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta miƙa wa ɗan wasan baya na ƙasar Ingila Trent Alexander-Arnold mai shekara 26, tayin kwantiragin shekaru biyar akan fam miliyan 78, yayin da Real Madrid ke zafafa nemansa. (Mirror)

Napoli ta fara tattaunawa da Liverpool da wakilin Federico Chiesa kan batun ɗaukar aron ɗan wasan mai shekara 27 na tsawon watanni shida. (Footmercato)

Paris St-Germain na shirin tattaunawa da Aston Villa kan batun musayar ɗan wasan Faransa Randal Kolo Muani, mai shekara 26, da ɗan wasan Colombia Jhon Duran, mai shekara 21. (Football Insider)

Ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee na son barin Manchester United, yayin da Juventus ke zawarcin ɗan wasan mai shekaru 23. (Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan United da Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, na jan hankalin ƙungiyar Seattle Sounders ta gasar Major League Soccer. (Teamtalk)

Liverpool na son ɗan wasan Bayern Munich da Jamus Leroy Sane, mai shekara 28, a matsayin wanda zai maye gurbin Mohamed Salah mai shekara 32. (Fichajes)

Wolves na daf da tsawaita kwantiragin ɗan wasan Brazil Matheus Cunha duk da cewa dan wasan mai shekara 25 ya kasance wanda Arsenal ke zawarci a kasuwar ƴan wasan watan Janairu. (Eduardo Burgos, Diario AS)

Ɗan wasan baya na Manchester United Tyrell Malacia, mai shekara 25, yana cikin jerin ƴan wasan da Juventus ke zawarci inda ta ke kallon ɗan ƙasar Holland ɗin a matsayin wanda zai maye gurbin gogaggen ɗan wasan baya na Brazil Danilo, mai shekara 33. (Daily Star)

Manchester City na shirin miƙa tayi kan ɗan wasan gaban Eintracht Frankfurt Omar Marmoush, mai shekara 25, a ƙoƙarin da ta ke yi na doke Arsenal da Tottenham da Liverpool wajen sayen ɗan wasan na Masar. (Footmercato)

Ipswich Town ta kammala yarjejeniyar ɗaukar aron ɗan wasan baya Ben Godfrey daga Atalanta. (Fabrizio Romano)

Bournemouth ta amince da cinikin ɗan wasan bayan Argentina Julio Soler, mai shekara 19, daga Lanus a kan farashin fam miliyan 12. (Uriel Lugt)

Real Betis na ci gaba da tattaunawa da Liverpool kan batun karɓar aron ɗan wasan tsakiyar Sifaniya Stefan Bajcetic, mai shekara 20. (Fabrizio Romano)