Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham ta tsawaita kwantiragin Son Heung-min
Tottenham ta tsawaita kwantiragin ƙyaftin, Son Heung-min zuwa shekara ɗaya, kenan zai ci gaba da taka leda a ƙungiyar zuwa karshen kakar 2026.
Mai shekara 32 ya koma Tottenham da murza leda daga Bayern Leverkusen a 2015, kawo yanzu ya ci ƙwallo 169 a wasa 431 a ƙungiyar.
Ɗan wasan tawagar Koriya ta Kudu ya ci ƙwallo 125 ya bayar da 68 aka zura a raga a karawa 320 a Premier League.
Yana cikin ƴan wasan da suka kai Tottenham wasan karshe a Champions League da karewa a mataki na biyar a bara a teburin Premier League.
Tottenham tana ta 12 a kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, kuma Son ya ci ƙwallo biyar ya bayar da shida aka zura a raga a karawa 17 a kakar nan.
Ƙungiyar da ke Arewacin Landan ta sanar da labarin tsawaita yarjejeniyar Son a lokacin da take shirin karawa da Liverpool a Carabao Cup zagayen daf da karshe ranar Laraba.