Vardy ya nemi afuwa kan faɗawar Leicester ralageshon

Jamie Vardy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jamie Vardy ya zura ƙwallo bakwai a cikin kakar wasa ta bana
    • Marubuci, Alex Brotherton
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Kyaftin ɗan ƙungiyar Leicester City ya bayyana halin da ƙungiyar ta samu kanta a wannan kaka a matsayin "mawuyaci" kuma "babban abin kunya" bayan faɗawar da ƙungiyar ta yi zuwa sahun gajiyayyu daga babbar gasar Firimiyar Ingila.

Shan kashin da Leicester ta yi da ci ɗaya da nema a hannun Liverpool ranar Lahadi ne ya tabbatar da cewa ƙungiyar ta faɗa ralageshon, lamarin da ke nufin sun faɗa ralageshon sau biyu a cikin kakar wasa uku da suka gabata.

Vardy ya ce: "Babu wasu kalamai da za su iya bayyana ɓacin raina da baƙin ciki kan halin da muka tsinci kanmu a wannan kaka. Ba mu da wani uzuru da za mu bayar," kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.

"Kasancewa ta a wannan ƙungiya, mun shiga halaye daban-daban da nasarori - amma a wannan kakar babu wani abu sai baƙin ciki, musamman gare ni, wannan babban abin kunya ne. Abin akwai cin rai, kuma na san cewa ku ma haka kuke ji.

"Ga magoya bayanmu: zan ce muku ina ba ku hakuri, ku yi haƙuri ba mu yi ƙoƙari ba."

Vardy na cikin tawagar da ta lashe gasar Firimiya a kakar 2015-16, kafin suka kai matakin kwata-fainal a Gasar Zakarun Nahiyar Turai a kakar 2016-17 tare da lashe kofin FA da Community Sheild a 2021.

Yanzu haka Leicester na a mataki na 19 a teburin Firimiya bayan samun maki 18 kacal a cikin wasa 33 da suka buga.

Ƙungiyar ta kasa taɓuka wani abin kirki duk da naɗin da ta yi wa Ruud van Nistelrooy a matsayin mai horaswa a watan Nuwamban 2024, inda a wannan karo suka kasa haɗa maki 34 jimilla kamar yadda suka samu a kakar baya da suka faɗa ralageshon.

Vardy ya buga wa Leicester wasa 496 tun bayan zuwa ƙungiyar daga Fleetwood Town a shekarar 2012.

A kakar wasa da ta gabata ya ci wa ƙungiyar ƙwallo 18 lokacin da ta lashe gasar Championship, amma a wannan kakar ƙwallo bakwai kawai ya iya zurawa a gasar Firimiya.