Aston Villa na son de Bruyne, Real Madrid na zawarcin Kerkez

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kevin de Bruyne
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Aston Villa ta tattauna kan yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Belgium, mai taka leda a Manchester City, Kevin de Bruyne mai shekara 33, wanda zai bar Etihad a kakar nan. (Sky Sports)

Leeds na duba yiwuwar korar Daniel Farke duk da Bajamushen ya yi kokarin maida kungiyar Premier League. (Mail)

Liverpool, da Real Madrid da Manchester City na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan baya na Hungary mai taka leda a Bournemouth, Milos Kerkez, mai shekara 21. (Sky Sports)

Manchester United na fafatawa da Chelsea da Real Madrid domin dauko matashin dan wasan tsakiya na Argentina, mai taka leda a River Plate, Franco Mastantuono, mai shekara 17, wanda aka yi wa farashin fam miliyan 38. (Mail)

Manchester United za ta yi zazzafar fafatawa da Arsenal da Aston Villa da wasu kungiyoyi 5 na Premier League kan dan wasan gaban Wolves, Matheus Cunha, mai shekara 25. (Sky Sports)

Al-Hilal ta saka dala miliyan 100, a kokarin sayan dan wasan gaban Brazil da Barcelona Raphinha, tare da bai wa dan wasan mai shekara 28 tayin kwantiragin shekara 4 da ya kai dala miliyan 200.(Sport - in Spanish)

Dan wasan gaban Portugal, mai taka leda a Chelsea, Joao Felix mai shekara 25, wanda ke zaman aro a AC Milan, ya fara tattaunawa kan komawarsa tsohon kulub din shi wato Benfica a lokacin bazara. (CaughtOffside)

An yi nisa a tattaunawa tsakanin Barcelona da kocinta Hansi Flick, mai shekara 60, kan sabuwar kwantiragi har zuwa shekarar 2027. (Sky Germany)

Dan wasan gaban Brazil Vinicius Jr, mai shekara 24, na matakin karshe na tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid. (Fabrizio Romano)

Arsenal na da kyakkyawan fata kan dauko dan wasan Sifaniya Martin Zubimendi, mai shekara 26. (CaughtOffside)