Tarihi da ƙuruciyar Kamala Harris

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Rachel Looker and Holly Honderich
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Kimamin sa'a ɗaya kawai bayan Joe Biden ya janye daga takararsa ne ƴan jam'iyyar Democrat suka koma bayan Kamala Haris domin ta yi musu takara a zaɓen na 2024.
A daidai lokacin da mataimakiyar shugaban ƙasar take neman zama shugabar ƙasa mace ta farko a ƙasar, yaƙin zaɓenta ya tattaro mutane masu sauƙin ra'ayi, sannan kwamitin yaƙin zaɓen ya samu tallafin dala miliyan 671m (£514m) a cikin wata biyu - kusan ninki uku na abin da abokin takararta na Republican Donald Trump ya tara.
Wannan ya sa muka yi nazarin rayuwa da tarihin ƴar takarar da muhimman abubuwan da suka faru a rayuwarta daga tasowarta har zuwa lokacin da ta samu tikitin zama ƴar takarar shugaban ƙasa.
Yadda Kamala ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa
Ms Harris ta fara siyasa ne shekara biyar da suka gabata.
Da farko ta fara aiki ne a matsayin babbar mai gabatar da ƙara ta yankin Alameda, sannan daga 2004 zuwa 2011 ta zama babbar lauyar San Francisco.
Daga baya ta samu ƙarin girma zuwa jihar California, inda ta zama mace ta farko kuma baƙar fata da ta zama babbar jojin jiha mafi shahara a Amurka.

Asalin hoton, San Francisco Chronicle/Getty Images
Daga lokacin ne ta yi takarar sanata mai wakiltar California. Sannan a shekarar 2020 ta shiga takarar shugaban ƙasa, amma takarar tata ba ta yi nisa ba. Daga baya sai Mista Biden ya ɗauko ta a matsayin mataimakiyarsa.
Gil Duran, tsohon daraktan watsa labarai na yaƙin zaɓen Harris ya bayyana cewa tana da ƙwarewa sosai.

Asalin hoton, Reuters
Ms Harris ta mayar da hankali kan wasu muhimman tsare-tsare, inda ake tunanin akwai sa hannunta a duk wata nasara da gwamnatin Biden ta samu.
Biden ya buƙaci Harris ta jagoranci ƙoƙarin gano abubuwan da ke jawo shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba ta kan iyakar Amurka da Mexico.
A ƴan kwanakin nan, Ms Harris ta sha nanata illolin da hana zubar da ciki suke jawowa, bayan Kotun Ƙolin ƙasar ta warware hukuncin Roe da Wade, wanda hukunci ne da ya fi shekara 25 yana tabbatar da haƙƙin zubar da ciki a 2022.
A jawabinta a wajen babban taron jam'iyyarsu, wanda shi ne babban taron da ta taɓa yin jawabi a rayuwarta, Ms Harris ta soki Trump da jam'iyyar Republican da shirya kutunguilar hana zubar da ciki a ƙasar, inda ta ce za ta dawo wa matan ƙasar da wannan ƴancin.

Asalin hoton, Getty Images
Ms Harris tana ƙara dagewa domin jawo hankalin masu kaɗa ƙuri'a domin samun nasara.
A kamfe na 2020, ta bayyana shirinta na samar da daidaito ga ƴan luwaɗi da maɗigo da sauran abubuwa.
Yanzu, kimanin shekara huɗu baya kuma, ta yi alƙawarin samar da tsare-tsaren da za su ɗaga darajar iyalai.
"A duk ayyukan da na yi a baya, mutane su ne nawa," in ji ta.
Asalin Kamala Harris
An haifa Harris ne a Oakland a jihar California. Mahaifiyarta ƴar asalin India ce, mahaifinta kuma ɗan asalin Jamaica ne.
Iyayenta sun rabu tana da shekara biyar, inda mahaifiyarta mai suna Shyamala Gopalan Harris ta ci gaba da kula da ita
Ms Harris ta taso ne tana cuɗanya da al'adun India, kasancewar tana yawan bin mahaifiyarta zuwa ƙasar.
"Mahaifiyata ta san cewa ƴaƴanta biyu mata ne kuma baƙaƙe. Ta san cewa ƙasar da take zaune za su riƙa kallon ƴaƴanta a matsayin baƙaƙen fata ne, wanda hakan ya sa ta ƙuduri aniyar ƙarfafa mana gwiwa."

Asalin hoton, Kamala Harris
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amma rayuwarta a jami'ar Howard, wadda ɗaya ce daga cikin manyan makarantu da baƙaƙen fata suke karatu ya sauya rayuwarta, inda ita ma ta ce zuwanta jami'ar ya matuƙar sauya mata rayuwa da tunani.
Lita Rosario-Richardson ta haɗu da Kamala Harris ne a jami'ar Howard a shekarun 1980 a wurin da ɗalibai suke taruwa suna tattauna batutuwa da suka danganci siyasa da kwalliya da sauran su.
Sai suka shaƙu saboda yadda suke da tunani iri ɗaya, da kuma kasancewar dukkansu sun taso ne a hannun iyayensu mata.
"A zamanin mulkin Reagan ne, inda ake tsaka da tattauna maganar batun ƴan Afirka mazauna Amurka da batun hotun Martin Luther King," in ji Ms Rosario-Richardson.
"Mun san cewa a matsayinmu na zuriyar mutanen da aka yi wa mulkin mallaka kuma baƙaƙen fata, ilimi ne kawai zai ba mu wata dama a cikin al'umma," in ji ta.
Amma ita Haris tana rayuwa cikin turawa cikin sauƙi. Ta yi rayuwa na wani lokaci a Canada lokacin da mahaifiyarta Ms Gopalan Harris ta yi aikin koyarwa a jami'ar McGill, inda Kamala da Maya suka bi ta can, har suka yi makaranta a Montreal na shekara biyar.
Harris ta shaida wa Washington Post a 2019 cewa bai kamata ana samun bambanci a tsakanin ƴan siyasa ba saboda bambancin launin fata.
"Ni dai ni ɗin ce, kuma ina alfahari da hakan," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa zauren muhawara a jami'a
Tun tasowarta take nuna alamun ƙwarewa, waɗanda su ne suke taimakonta samun nasarori, kamar yadda ƙawarta Ms Rosario-Richardson ta bayyana.
"Wannan ya jawo hankalin zuwa gare ta a lokacin da muka shiga zauren tattaunawa a jami'ar Howard," in ji ta.
A wani bidiyo da ta wallafa a shafukanta na sadarwa a 2020 bayan sun ci zaɓe, ta ce, "mun samu nasara Joe, kai ne shugaban ƙasar Amurka na gaba."
Yanayin dariya da murmushin da ta yi ne ya jawo hankalin ƙawarta, inda ta ce, "haka take da yawan dariya ko a zauren muhawararmu lokacin muna jami'a."
Kamala, 'Momala', mai kafa tarihi
A shekarar 2014, Harris lokacin tana sanata ne ta auri Doug Emhoff wanda lauya ne, inda ta ci gaba da riƙe yaransa biyu Cole and Ella.
Ta rubuta wata maƙala a mujallar Elle a sherara 2019, inda a ciki ta bayyana yadda ta zama mai kula da ƴaƴan.
"Da muka yi aure da Doug, sai ni da Cole da Ella muka amince cewa ba za su daina kirana da 'kishiyar uwa ba'. Sai suka fara kira na da 'Momala."
An ga Cole da Ella da mahaifinsu duka a babban taron jam'iyyar democrats a 2024, inda aka riƙa kiran su da "iyalai masu zaman aminci."
Ƙanwarta, Maya da ƴaruwarta, Meena ma duk sun zo babban taron.
Nadia Brown, ƙaramar farfesan nazarin siyasa a jami'ar Purdue ta shaida wa BBC cewa Kamala Harris na bin sahun Fannie Lou Hamer da Ella Baker da Septima Clark ne da sauran su.












