Barcelona na iya raba gari da Olmo, Real Madrid na son Van de Ven

Dani Olmo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan gaban Barcelona Dani Olmo, mai shekara 26, a shirye yake ya koma gasar Premier a watan Janairu idan kulob ya gaza yi wa ɗan wasan na Sifaniya rijista a zango na biyu a kakar wasan bana. (TBR Football)

A halin da ake ciki ƙungiyar ta La Liga, tana ƙoƙarin samun kuɗaɗen da za su ba ta damar yi wa Olmo rajista - matakan da suka haɗa da rage farashin da ta ke nema kan ɗan wasan tsakiyar Holland Frenkie de Jong, mai shekara 27. (Mundo Deportivo)

Real Madrid na zawarcin ɗan wasan bayan Tottenham da Netherlands Micky van de Ven, mai shekara 23 a watan Janairu, sakamakon raunukan da ƴan wasan bayan ƙungiyar ta Sifaniya ke fama su. (Relevo)

Sai dai tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar Sergio Ramos, mai shekara 38, wanda a halin yanzu ya ke zaman kansa yana son komawa Real Madrid sakamakon ƙalubalen da ƙungiyar ke fusakanta inda ɗan wasan sifaniya, mai shekara 32, Dani Carvajal, da ɗan Austria David Alaba, mai shekara 32, da ɗan Brazil Eder Militao, mai shekara 26 duk su ke fama da raunuka. (AS)

Ɗan wasan baya na ƙasar Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, bai shaidawa Liverpool cewa ya zaɓi komawa Real Madrid a kyauta a bazara mai zuwa ba, duk da rahotanni daga Sifaniya na cewa an yi hakan. (Liverpool Echo)

Ɗan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 30, ba ai tunanin rage zaman aron da ya ke yi a Arsenal daga Chelsea a watan Janairu ba, duk da cewa bai fara wasan Firimiya ba tun ranar 19 ga Oktoba. (Athletic)

Har yanzu Everton ba ta fara tattaunawa da ɗan wasan bayan Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22 kan sabuwar kwantiragi ba, wanda Liverpool da Manchester United da Manchester City ke zawarcinsa. (Daily Mail)

Liverpool na sa ido kan halin da ɗan wasan baya na Fulham, Antonee Robinson ke ciki, kuma za ta iya miƙa tayi kan ɗan wasan bayan na Amurka, mai shekara 27, a watan Janairu.(Football Insider)

Real Madrid na shirin fara tattaunawa da ɗan wasan gaban Brazil Vinicius Jr, mai shekara 24, kan sabuwar yarjejeniya. (AS)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester City Kevin de Bruyne, mai shekara 33, ya fi son komawa gasar Major League Soccer ta Amurka, idan ɗan ƙasar Belgium ɗin ya bar ƙungiyar idan kwantiraginsa ya ƙare a bazara. (Teamtalk)

Tsohon ɗan wasan Manchester City Mario Balotelli, mai shekara 34, na jan hankalin ƙungiyar Cruz Azul ta Mexico - wanda za ta zama kulob na 13 da ɗan Italiyan zai bugawa. (Gazzeta dello Sport)