Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Biyan kuɗin Inshora na tayar da hankalin Amurkawa fiye da neman abinci
- Marubuci, Natalie Sherman & Brandon Drenon
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Matsanancin yanayi da ake fuskanta na tilasta masu ba da Inshorar gida a Amurka na barin harkar gaba ɗaya, yayin da hakan ya jefa da yawansu cikin halin matsin rayuwa.
Gretchen Bradford ta yanke shawarar ba za ta biya inshorar gida na bana ba.
Ƴar shekaru 59 ta rayu gaba ɗaya rayuwarta a New Orleans, wanda ke kusa da Tekun Louisiana, yankin da fama da sauyin yanayi da gagarumar guguwa.
Tana zama ne a gidan da iyayenta suka saya a shekarar 1958, sai dai tana fuskantar ƙarin inshora duk shekara.
A shekarar 2021, ta biya dalar Amurka dubu 3,035, yayin da 2022 kuɗin suka linku har sau uku wato dalar Amurka dubu 9,876, adadin da ba za ta iya biya ba.
"Biyan Inshora a wajena daidai yake da daina cin abinci a yanzu, saboda rayuwata ta ta'alaƙa ne kan inshorar da ke ba masu lalura ta musamman," Inji Ms Bradford.
"Ba zan iya shuka bishiyar kuɗi ba. bani da su, saboda haka ban san yadda zan yi ba."
To sai dai ba Misis Bradford kaɗai ce ke fuskantar irin wannan ƙalubale ba.
A duk faɗin ƙasar ana fuskantar hauhawar kuɗin Inshora, yayin da masana kimiyya ke danganta hakan da sauyin yanayi da ke fuskanta.
Da yawan ƙananan kamfanonin inshora sun rufe saboda kasa fuskantar matsalar biliyoyin daloli da harkar ke fama da ita.
A wasu jahohi da ke fama da matsananciyar guguwa ko wutar daji da kuma ambaliyar ruwa kamar irin su California, da Florida da Louisiana.
Kamfanoni sun ce matsalar na ƙamari ne saboda illar da sauyin yanayi ke haifarwa a yankunan, wanda hakan ne ya sa kuɗin ke ninkuwa duk bayan wani ɗan lokaci.
A duk faɗin ƙasar, ana tsammanin ƙimar kuɗi za ta ƙaru da kashi tara cikin ɗari, bayan ya ƙaru da kashi bakwai a shekarar 2022.
To sai dai yankunan da ke fuskantar haɗarin sauyin yanayi sun fi fuskantar ƙarin kuɗaɗen inshora da kusan dalar Amurka dubu 5,000 a kowace shekara wato sama da kashi 65 cikin ɗari tun daga shekarar 2021.
Wani mazaunin garin Louisiana, Teddy Mars, ya ce ya cire dala dubu 12,000 daga asusun ajiyarsa na ritaya a watan da ya gabata don taimakawa wajen biyan inshoransa.
Mutumin, mai shekaru 44, ya ce sai dai ya nemi wani kamfanin inshorar ya sake rajista da shi saboda kamfaninsa na asali ya bar jihar gaba ɗaya saboda yanayin matsi da ake fuskanta.
"Ba za mu iya ɗorewa ba, wani lokaci na kanji kamar na sayar da gidan saidai ina tunanin waye zai sayi gida a yanzu idan ba shi da halin biyan inshora?"
Iyalan sun rage abin da suke kashewa ga abinci da tufafi, saboda suna zama da yaronsu da ya fara tasawa, saboda haka ya ce suna kashe fiye da abin da suke samu a matsayinsu na ma'aikata shi da matarsa a fannin ilimi.
Kadarori na cikin hatsari
Sakamakon hauhawar ƙudin inshora, ana sa ran kasuwar saye da sayarwar kadarori ka iya fuskantar barazana a Amurka, kuma zai rage yawan buƙatar mallakar gidaje a jihohin da ke fuskantar matsalar wutar daji da tsananin zafi da matsanciyar guguwa, a lokaci guda farashin gidajen ya faɗi ƙasa warwas.
To amman abin tambaya shi ne, waye zai biya ɓarnar da sauyin yanayi ya haifar?
Shin sauyin yanayi ne ke haifar da fari da tsananin zafi da wutar daji da kuma ambaliya?
"Ba a taɓa samun lokaci a Amurka da za a ce babu tabbas ba kamar yanzu," inji Jeremy Porter, shugaban bincike kan tasirin yanayi na Gidauniyar First Street, mai zaman kanta, wanda ke nazarin haɗarin sauyin yanayi.
"Ba mu san yanayin ya yi ƙamari ba sai yanzu, amma mutane sun fara fahimtar haɗarin da ke tattare da sauyin yanayi sun kuma sun fara yin la'akari da hakan."
Yanayin yadda sauyin yanayi ke ƙara ƙamari a wasu sassan, nan da wasu shekaru masu zuwa akwai yiwuwar a fuskanci gagarumar barazana, ya danganta da inda lamarin zai faru da kuma lokacin da zai faru.
Yadda ake barin Louisiana
A garin Louisiana, darajar kadarori na raguwa fiye da sauran sassan Amurka, saboda ƙarin inshora da yankin ke fuskanta.
Tsakanin shekarar 2020 da 2022, yawan al'umar yankin ya ragu matuƙa lamarin da ake alaƙantawa da hauhawar kuɗin ishora da yankin ke fama da shi.
Tyler Coats, ya sayi gida a New Orleans a shekarar 2011, sai dai daga bisani ya koma Arkansas afarkon shekarar 2020 saboda fargabar ambaliyar ruwa.
Tyler Coats, mai shekara 36, yana da ƙaramar sana'a a garin Big Easy bayan ya kammala jami'a, yanajin daɗin rayuwarsa idan dare ya yi, ya kuma samu ƙwarin guiwar taimakawa wajen sake gina birnin bayan ɓarnar da guguwa mai tafe da iska ta Hurricane ta yi.
Sai dai bayan ya yi aure ya haihu, ya ce ya fuskanci wasu abubuwa daban na rayuwa.
"Duk shekara ana fuskantar wannan guguwar ta hurricane, kuma bakasanin ko zaka iya rasa duk wani abu da mutum ya tanada na kasuwanci, bansan hakan za ta ci gaba da faruwa ba shiyasa na sayi gida tun farko." inji Coats.
Mista Coats ya ce baya kewar garin da ya bari, saboda inda yake rayuwa yanzu yana biyan ishora ƙasa da yadda yake biya a baya kuma gidansa na yanzu ya fi girma.
Masu gidajen da suka kasa tashi ko sauya wuri basu da tabbacin lokacin da sauƙi zai samu.
Ƴan majalisar yankin sun amince da samar da dala miliyan 45 domin taimakawa kamfanonin Inshora ta hanyar raba hasara, a ƙoƙarin hukumomi na daidaita al'amurra da matsin da guguwar Hurricane Katrina ta haifar a shekarar 2005.
A ɓangaren Misis Bradford, ta ce ba za ta taɓa sayar da gidanta da ke wajen shaƙatawa na Pontchartrain ba, saboda an saka wurin cikin jerin wuraren tarihi na ƙasa.
Sai dai matakin da ta ɗauka na ci gaba da zama a yankin ya sakata cikin fargaba da tsoron abin da ka iya faruwa nan gaba.
Mista Porter na gidauniyar 'First Street', ya ce akwai buƙatar gwamanati ta zauna da kamfanonin inshora wajen ganin ta shawo kan matsalar.