BBC za ta gudanar da muhawara da 'yan takarar Gwamna a Kaduna

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
An wallafa

A ranar Laraba ne 18 ga watan Janairun 2023 ne BBC za ta gudanar da muhawarar ƴan takarar gwamna a Kaduna.

Cikin ƴan takarar da za su yi muhawarar akwai Uba Sani na Jam'iyyar APC da Isa Mohammad Ashiru na Jam'iyyar PDP.

Haka kuma akwai Suleiman Othman Hunkuyi na Jam'iyyar NNPP da kuma Sani Mohammad Sha'aban na ADP.

Za ku iya kallon wannan muhawara kai tsaye a shafinmu na Facebook BBC Hausa Facebook da YouTube.