Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta ɗauki Hojbjerg, Al-Ittihad ta matsa kan ɗaukar Salah
Manchester United na nazarin shammatar mutane, ta ɗauko ɗan wasan tsakiyar Denmark mai shekara 28, daga Tottenham Pierre-Emile Hojbjerg. (Telegraph)
Al-Ittihad na shirin jarraba imanin Liverpool, wadda ta dage cewa ɗan wasan gaban Masar, Mohamed Salah ba na sayarwa ba ne, inda za su gabatar wa Liverpool tayin dala miliyan 162, don ɗan ƙwallon mai shekara 31. (CBS Sports)
Manchester United ta fara tuntuɓa game da ɗan wasan bayan Ingila na kulob ɗin Brentford Rico Henry, mai shekara 26, yayin da suke tunani a kan zaɓin maye gurbin ɗan ƙwallon bayan Ingila Luke Shaw, mai shekara 28 da ya ji rauni. (Mail)
Sai dai United ta shirya ƙin amincewa da tayin baya-bayan nan daga West Ham a kan ɗan wasan bayanta na Ingila, Harry Maguire, mai shekara 30, wanda koci Erik ten Hag, ke son ganin ya ci gaba da zama a kulob ɗin mai fama da matsalolin raunin 'yan wasa. (talkSPORT)
Chelsea na tunanin yin wani yunƙuri a makare na ɗauko ɗan ƙwallon tsakiyar Ingila mai shekara 23 daga kulob ɗin Arsenal, Emile Smith Rowe, da 'yan wasan Barcelona biyu - na farko ɗan ƙwallon gaba na Sifaniya mai shekara 23, Ferran Torres, da ɗan wasan gefen Brazil, Raphinha, mai shekara 26. (Mail)
Tottenham sun shiga tattaunawa da Nottingham Forest a kan wata yarjejeniya game da ɗan wasan gaban Wales, Brennan Johnson, amma dai har yanzu ba ta gabatar da tayi a ƙa'idance a kan ɗan wasan mai shekara 22 ba. (Sky Sports)
Barcelona na sa ran kammala wata yarjejeniya ta ɗauko aron ɗan ƙwallon bayan Manchester City na ƙasar Portugal mai shekara 29, Joao Cancelo, nan da 'yan kwanaki. (ESPN)
Nottingham Forest na ƙara matsawa daf da ɗauko ɗan wasan tsakiyar Leicester na Najeriya mai shekara 26, Wilfred Ndidi. (talkSPORT)
Sai dai Bayern Munich ma na sha'awar samun Ndidi. (Football Insider)
Liverpool na matsa lamba don sayo ɗan ƙwallon gefe na Belgium mai buga wa PSV Eindhoven Johan Bakayoko, wanda ƙungiyoyin Everton da Burnley har ma da Crystal Palace duk suke nuna sha'awa a kan ɗan wasan mai shekara 20. (Football Insider)
Nottingham Forest sun gabatar da tayin kusan yuro miliyan tara don sayen golan Benfica, ɗan ƙasar Girka, Odysseas Vlachodimos, mai shekara 29. (Fabrizio Romano)
Forest ɗin sun kusa kammala musayar ɗan ƙwallon tsakiya na Argentina mai shekara 25, daga kulob ɗin Bologna, Nicolas Dominguez, yayi da ɗan wasansu na tsakiya daga ƙasar Switzerland Remo Freuler, mai shekara 31, zai koma can. (Sky Sports)
Leeds ta tunkari Tottenham don ɗan wasanta na baya mai shekara 23 daga Ingila, Djed Spence, a kan wata yarjejeniyar aro tsawon kakar wasanni guda. (Athletic)
Ƙungiyar ƙwallon Saudiyya, Al-Ittihad tana kuma da sha'awar ɗaukar ɗan ƙwallon baya na Ingila mai buga wa Liverpool, Joe Gomez, sai dai kulob ɗin na Liverpool ya ce ba shi da niyyar sayar da ɗan wasan mai shekara 26. (Fabrizio Romano)
Ɗan ƙwallon tsakiyar Brazil Fred mai shekara 30, ga alama ya tabbatar da yiwuwar tafiyar golan Turkiyya mai shekara 25, Altay Bayindir zuwa Manchester United ta hanyar yi wa takwaran nasa na kulob ɗin Fenerbahce bankwana. (Manchester Evening News)