Dan wasan Arsenal, Tierney ya koma Sociedad

An wallafa

Dan wasan baya na Arsenal Kieran Tierney ya koma Real Sociedad ta gasar La Liga a matsayin aro na tsawon kakar wasa daya.

Dan wasan na Scotland mai shekara 26 ya koma Gunners ne a kan fam miliyan 25 daga Celtic a shekarar 2019.

Tierney ya buga wasa sau 124 a kulob din, inda ya ci kwallo biyar.

Wasanni shida ne kawai ya fara a gasar Premier a kakar wasan da ta gabata yayin da Arsenal ta kare a matsayi na biyu, kuma ba a tunanin dan wasan na cikin tsarin Mikel Arteta na wannan kakar.

An cire Tierney daga cikin ‘yan wasan da za su buga wasanni uku na farko na Arsenal a kakar wasa ta bana, duk da cewa ya buga wasa a matsayin wanda ya shigo daga baya a gasar Community Shield da suka doke Manchester City a farkon watan nan.