'Cutar laka ba ta hana ni cimma burina na zama wani abu ba'

An wallafa

Ahmed Salami mai shekara 18 ya dade yana mafarkin yadda zai shahara. An haife shi da cutar laka kuma sai da ya shekara shida sannan ya fara magana, ita din ma cikin in'ina.

a yanzu da taimakon mahaifiyarsa, duk mako sai ya wallafa bidiyo a Youtube don aika sakon kwarin gwiwa ga masu lalurar nakasa.