Man Utd ta kawo karshen zawarcin Kane, Chelsea za ta yi gogayya da Arsenal a kan Caicedo

Asalin hoton, OTHER
Manchester United ta kawo karshen zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 29 daga Tottenham a kakar bana. (Guardian)
Newcastle ta kusa kammala amincewa da yarjejeniyar fan miliyan 50 tare da Inter Milan a kan dan wasan tsakiyar Italiya Nicolo Barella. (Telegraph)
Arsenal na kan gaba wajen daukar Kai Havertz daga abokiyar hamayyarta ta London Chelsea wadda ta bukaci fan miliyan 70 a kan dan wasan mai shekara 24. (Guardian)
Juventus na son akalla yuro miliyan 80 a kan Dusan Vlahovic, to amma Chelsea ta fada mata cewa za su iya daukar ‘yan wasa tsakanin biyar a matsayin musaya a kan dan wasan gaban Serbian. (Gazzetta dello Sport daga Football Italia)
Ita kuwa Inter Milan na son ‘yan wasan da suka hada da Kalidou Koulibaly, tare da dan bayan Senegal mai shekara 31. (Corriere dello Sport)
Manchester City ba za ta yarda ta bayar da aron dan wasan tsakiyar Ingila James McAtee, wanda suke so su sa shi a jerin ‘yan wasan da za su buga musu tamola a kaka mai zuwa ba. (Mail)
Chelsea kuwa a shirye take ta yi gogayya da Arsenal wajen siyen dan wasan Brighton Moises Caicedo, yayin da Bayern Munich kuma ke son dan wasan. (Football Insider)
Mai tsaron ragar Sifaniya David Raya mai shekara 27, ya amince ya koma Tottenham. (Fabrizio Romano)
Nottingham Forest ta ki yarda da tayin da aka yi wa dan wasanta Brennan Johnson mai shekara 22 daga Brenford. (Sky Sports)
Burnley da Bournemouth na kan gaba wajen siyan dan gaban Mali El Bilal Toure, mai shekara 21 daga Almeria a kakar bana . (Football Insider)














