Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chelsea ta kammala cinikin Wiley daga Atalanta United
Chelsea ta sanar da kammala cinikin ɗan ƙwallon tawagar Amurka, Caleb Wiley.
Mai tsaron baya ya koma Stamford Bridge daga Atlanta United, ya kuma sa hannu kan ƙunshin yarjejeniyar kaka shida da cewar za a iya kara masa shekara ɗaya.
Wiley ya fara taka leda a makarantar koyon tamaula ta Atlanta yana da shekara 11 da haihuwa.
Daga nan ta kai da ya shiga cikin manyan ƴan wasan ƙungiyar, wanda ya wakilci Atlanta tun daga kakar 2020 da kuma 2021 a karamar gasar tamaula ta Amurka.
Mai shekara 19 ya taka rawar gani a Atlanta a kakar 2022, ciki har da cin ƙwallo a wasan da suka doke Sporting Kansas City 3-1 - daga nan ya yi wasa 25 a kakar.
Ɗan wasan yana cikin matasan da za su buga wa Amurka gasar Olympic a fannin ƙwallon kafa da za a yi a birnin Paris a makon nan.
Wiley ya buga wasa 36 a kakar 2023 a babbar gasar tamaula ta Amuurka, wanda ya fara da fuskantar Mexico cikin Oktoba da suka tashi 1-1.
Ya zama mai buga wa Atlanta wasa sosai, wanda ya yi karawa 23 a dukkan fafatawa a kakar da ta wuce.