Ten Hag ya yi martani kan kalaman Carragher

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Manchester United Erik ten Hag ya mayar da martani ga sukar tsohon dan wasan Liverpool Jamie Carragher ya yi kan dabarunsa a wasan da Fulham ta doke United da ci 2-1.
Carragher ya soki yadda United ta yi wasa a ranar Asabar yayin da ya ke zantawa da manema labarai.
Ten Hag ya yarda cewa kalaman tsohon mai tsaron bayan Liverpool ɗin na da "ma'ana" amma ya ce daman tun farko da niyyar suka ya zo.
Carragher ya yi nuni da yadda United ta ke "tsare baya kamar ƙungiyar da ban taɓa gani ba" inda suka bar babban giɓi a tsakiyar filin da Fulham ta yi amfani da shi wurin samun nasararta ta biyu a Old Trafford tun 1963.
Ten Hag ya ce: "Wataƙila a cikin rabin sa'a na farko, ya faɗi gaskiya. Fulham ta mamaye mu da yadda ta shirya ƴan wasanta na tsakiya kuma dole ne mu nemo mafita. Amma bayan rabin sa'an ta farko mun magance lamarin.
A wata hira da MUTV, Ten Hag ya ƙara da cewa Maguire ba zai buga karawar da za su yi da Forest ba saboda rauni, yayin da kuma akwai shakku kan lafiyar Raphael Varane da kyaftin Bruno Fernandes.








