Bikin al'adun Afirka da mai kiwon zomo a cikin hotuna

Yara

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wasu 'yan makaranta a Zimbabwe ke motsa jiki a lokacin bikin zagayowar samun 'yancin kan ƙasar da aka yi ranar Talata.
An wallafa
Yara

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Laraba kuma 'yan asalin Afirka mazauna Panama suka sanya tufafin Afirka a bikin rawar al'adun ƙasar Kongo.
mm

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi a birnin Johannesburg, na ƙasar Afirka ta Kudu, wata gidauniya ta shirya dafa abinci domin bayar wa ga mabuƙata a lokacin watan azumi.
cc

Asalin hoton, ANADOLU AGENCY

Bayanan hoto, Mercy Munene ke ɗauke da zomo daga cikin ɗaruruwan zomaye da take kiwo a gonar kiwon zomayenta da ke wajen Nairobi babban birnin ƙasar Kenya
d

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A garin Giza na arewa da kogin Nilu, an kunna fitilu domin alamta ƙarewar watan Ramadan.
s

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Talata bayan da aka samu mummunar ambaliya, mutane na ƙoƙarin fita zuwa kasuwancinsu a Luanda babban birnin Angola.