Yaya Birtaniya ke zaman makokin sarakunanta?

Asalin hoton, Getty Images
Kamar duk wani abu da ya shafi iyalan masarautar Burtaniya, mutuwar basarakiyar ma ya kunshi wasu abubuwan al'adu da kuma taruka da za a yi.
Bayan mutuwar sarauniya Elizebeth ta biyu a ranar 8 ga watan Satumba, an ayyana iya lokacin da za a yi zaman makoki in da za a shafe kwanaki bakwai bayan jana'izarta.
Ga tarihin yadda ake gabatar da wasu al'adu na jimamin mutuwar sarauniyar wadda ta fi kowa dadewa a tarihin masarautar Burtaniya, wadansu daga cikin al'adun sun shahara a duniya.
Ana yin ƙasa-ƙasa da tutoci

Asalin hoton, EPA
Hanya ta farko da ake fara nuna ana zaman makokin a hukumance ita ce yin ƙasa-ƙasa da tutoci a duk wasu gine-ginen gwamnati da kuma gidajen sarauta a fadin Burtaniya.
Yayin da ake amfani da kalmar cewa an rage tsawon tuta da rabi, ainihin abin da ake yi shi ne ana dan sassauta ne a jikin karfen da ke rike da ita.
Hakan dadadiyar al'ada ce da aka yi tun karni na 17 na tsawon tuta.
An fara yin wannan al'ada ce a matsayin nuna girmamawa da jimami na mutuwar wani babban jami'i a jirgin ruwa.
Sauran ma'aikatan jirgin sai suka yi kasa kasa da tutar da ke jikin jirgin don nuna alhininsu a kan mutuwar jami'in na su.

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa wancan matakin bai shafi amfani da mayafin alamar Royal Standard na masarautar Burtaniya, kadawar tuta na alamta tabbatuwar 'yanci.
Za a yi ƙasa da ƙasa da sauran tutocin da ke Burtaniya har zuwa karfe 8 na safiyar wayewar garin da aka yi jana'izar sarauniya in ban da ranar 10 ga watan Satumba da majalisar masu nadin sarki ta ayyana Charles a matsayin sabon sarki.
A wannan rana an daga tutoci sama a kasar na tsawon sa'oi, kafin daga bisani a sake yin kasa kasa da su.
Harba bindiga

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wata al'ada da ake yi a yayin zaman makokin gidan sarautar Burtaniya ita ce harba bindigar ban girma.
A cewar masana tarihin rundunar sojin Burtaniya, an fara wannan al'ada ce a karni na 15 a lokacin da jiragen ruwa na yaki suka riƙa kai bindigogi gabar tekun kasashen waje abin da ke nuna cewa suna zuwa ne da kyakkyawar niyya domin babu komai a cikin makaman nasu.
A 1730, sai sojojin ruwan masarauta suka fara amfani da harba bindiga don murna ko jimamin wani muhimmin abu, ko da yake bai zamo wajibi ba ga iyalan masarautar kasar d ama sauran shugabannin kasa har sai zuwa 1808.
Akwai dokoki a kan adadin harbi nawa za a yi, domin ya danganta ne daga in da za a harba ta da kuma dalilin da ya sa za a harba ta.
A 1827, aka bayar da umarnin cewa harba bindiga sau 41 ya yi dai dai da nuna ban girma ga masu sarauta.
To amma a wasu lokuta ko kuma a wasu wuraren an kara yawan adadin harbin da za ayi zuwa 62.
An harba bindiga don nuna jimamin mutuwar mutuwar sarauniya Elizebeth da kuma lokacin da aka ayyana sarki Charles a matsayin wanda ya gaji sarauniya.
A washe garin rasuwar sarauniya wato ranar 9 ga watan Satumba, an harba bindigar ban girma sau 96 a wajen shakatawa na Hyde, in da duk harbi guda a matsayin shekararta guda.
Kaɗa ƙararrawa

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Ana amfani da wata takaitacciyar sanarwa da ake rubutawa a takarda a jikin wani dan karamanin allo don sanar da abubuwan da suka shafi ranakun haihuwa da kuma mutuwa a fadar ta Buckingham.
Ana makale allon ne a jikin karafan da ke kofar shiga fadar.
An sanar da mutuwar George na VI a 1952 da kuma George na V a 1936, ta wannan hanya.












