Kotu ta yi sammacin tsohon mataimakin shugaban Amurka

An wallafa

Kotu a Amurka ta tura wa tsohon mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence sammaci domin ya bayyana a gabanta saboda ya bayar da shaida kan binciken da ake yi wa tsohon shugaban ƙasa Donald Trump.

Sammacin na da alaƙa da yunƙurin Donald Trump na kawo ruɗani ga sakamakon zaɓen Amurka na 2020 bayan ya sha kaye.

Haka nan kuma lauyan ma’aikatar shari’a, Jack Smith na binciken Trump kan abin da ya shafi takardun sirri na ƙasa.

Wannan sammaci zai ƙara matsi a kan Mr Pence kasancewar yana yunƙurin ƙalubalantar Donald Trump a takarar shugabancin Amurka a 2024.

Rashin martaba sammacin zai iya janyo masa cikas a ɓangaren shari’a.

Sai dai har yanzu babu ɗaya daga cikin Mr Pence ko Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da ya tabbatar da batun sammacen.

Wannan wani muhimmin mataki ne a binciken da ake yi na tsawon shekara biyu game da lamarin da ya faru bayan babban zaɓen na Amurka.

A wancan lokaci shugaba Trump ya matsa wa mataimakinsa kan ya yi duk mai yiwuwa domin ganin ya yi zagon kasa ga shirin miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Joe Biden.

Sai dai turjewar da ya yi ta janyo har Donald Trump ya soke shi, kuma magoya bayan Trump din suka rinƙa neman a ‘rataye Mike Pence’.

Rahotanni na cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar na yunƙurin ƙaddamar da shirinsa na takarar shugaban ƙasa a 2024.

Tuni dai Donald Trump ya ƙaddamar da nasa yaƙin neman zaɓen.