Manchester United na tattaunawa da Evans

An wallafa

Manchester United na ci gaba da tattaunawa don siyan dan wasan baya na Northern Ireland Jonny Evans, in ji kocin Erik ten Hag.

Evans, mai shekara 35, ya koma United ne a kan dan gajeren wa’adi a watan da ya gabata domin buga wasannin share fage na kungiyar.

Yanzu dai yarjejeniyar ta kare, kuma yayin da tafiyar Harry Maguire zuwa West Ham ta ci tura, Ten Hag ya ce United na tattaunawa kan kawo Evans kan yarjejeniyar dindindin.

Evans ya buga wa United wasanni 198 kafin ya bar kungiyar a shekarar 2015, bayan da ya lashe kofin zakarun Turai da na Premier League uku.

Dan wasan bayan, wanda ya buga wa Northern Ireland wasa 102, ya shafe shekaru uku a West Brom, ya yi shekara biyar a Leicester kafin ya bar Foxes a karshen kakar wasa ta bara.

Evans ya buga wasannin sada zumuncin da United ta buga da Lyon da Wrexham da Borussia Dortmund da kuma Athletic Bilbao, sannan ya kalli wasan da suka doke Wolves a gasar Premier ranar Litinin daga wurin zaman daraktoci a Old Trafford.