Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Farfaɗowar darajar Naira, barazana ga shugaban NNPCL, karin kudin fetur
Yayin da muke ban kwana da wannan makon, mun duba muku wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya.
Darajar Naira ta fara farfaɗowa a kasuwa - Za ta ɗore ko kuwa?
A makon da ya gabata ne darajar kuɗin Najeriya ta naira ta ɗan farfaɗo da kusan kashi 22 cikin 100 a kwana uku idan aka kwatanta da faɗuwar da ta dinga yi da kashi 36.52 cikin 100 a shekarar 2022.
Ɗan kasuwar canji a Kano, Sani Dada, ya shaida wa BBC Hausa cewa kasuwar canji ta bayan-fage ta tashi a ranar Alhamis ana canzar da dalar Amurka ɗaya tsakanin N750 zuwa N760 a Kano.
A makon da ya gabata, an canzar da dala ɗaya kan N890 a kasuwar da ba ta hukuma ba, yayin da farashin bai wuce N439 ba a farashin gwamnati.
Soludo ya ta da ƙura game da ikirarin Peter Obi na zuba jari a Anambra
A makon da ya gabata ne kalaman da gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo, ya yi kan ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar Labour Peter Obi, sun tayar da ƙura da muhawara musamman a kafofin sada zumunta na ƙasar.
Soludon dai ya yi maratani ne a kan ikirarin da Mista Obi ke yawan yi a wuraren yaƙin neman zaɓensa inda yake kafa hujja da ɗumbin zuba jarin da ya yi a jihar daga tsakanin shkarar 2006 to 2014 lokacin yana gwamna.
A wata hira da Soludo ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce, “Ban san da wani labarin zuba jari ba. Hirarmu a kan kasafin kudin 2023 ce.
“Ba zan yi magana a kan batun zuba jarin magabatana ba. Kuma ma ni ban san komai a kan shi wannan zuba jarin da ake magana akai ba,” in ji gwamnan.
Ce-ce-ku-cen da muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa ta haifar a Najeriya
A makon da ya gabata ne gidan talabijin na Arise ya shirya wa ‘yan takarar shugabancin kasa a Najeriya da haɗin-gwiwar cibiyar bunƙasa harkokin dimokuraɗiya ta CDD.
Batun tsaro da tattalin arziki ne suka kasance manyan batutuwa da aka tafka muhawara a kansu.
Taron da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya, ya samu halartar masu neman kujerar shugaban kasa irinsu ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi; Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP da Kola Abiola na PRP.
Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da Bola Tinubu na APC da ake gani a matsayin manyan ‘yan takarar ba su halarci muhawarar ba, amma Atiku ya tura mai yi masa takarar mataimaki, gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa domin ya wakilce shi.
Me ya sa ake yi wa shugaban NNPC barazanar halaka shi?
A makon da ya gabata shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Malam Mele Kyari ya ce ya fuskanci barazana mai yawa ta neman halaka shi daga wasu mutanen da ba sa jin daɗin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kamanta gaskiya a hada-hadar mai da hana satar ɗanyen mai da ke haddasa asarar kudin-shiga ga gwamnati.
Malam Kyari ya faɗi hakan ne a wajen wani taro da majalisar wakilan ƙasar ta shirya, inda ya ƙara da cewa gaskiya rigar-ƙaya ce kamar yadda ƴan magana kan ce.
Kuma wannan ne ya sa suke fuskantar kalubale tun lokacin da suka duƙufa wajen aiwatar da wasu sauye-sauye a kamfanin man ƙasar da nufin kamanta gaskiya a hada-hadar kamfanin, wato NNPCL da ƙoƙarin hana satar danyen mai.
Abin da ya sa IPMAN ke son a yi karin kuɗin fetur a Najeriya
A makon da ya gabata Kungiyar dilallan man fetur ta Najeriya, IPMAN, ta bukaci a yi karin kudin man fetur a hukumance muddin ana so a saukaka wahalhalun samun mai da kuma kawo karshen karancinsa a faɗin kasar.
IPMAN ta yi wannan kira ne a daidai lokacin da ‘yan kasar ke cigaba da fuskantar karancin mai a galibin jihohin arewa da babban birnin tarayyar ƙasar, Abuja.
An kwashe 'yan makonni ana fama da karancin man fetur, duk da irin matakan da gwamnati ke cewa tana ɗauka domin saukaka matsalar.
Kusan tun a farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci ba a daukar wani dogon lokaci ba tare da an faɗa cikin karancin fetur ba a Najeriya.