Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ce-ce-ku-cen da muhawarar ‘yan takarar shugaban kasa ta haifar a Najeriya
Batun tsaro da tattalin arziki ne suka kasance manyan batutuwa da aka tafka muhawara a kansu a taron da gidan talabijin ta Arise ya shirya wa ‘yan takarar shugabancin kasa a Najeriya da haɗin-gwiwar cibiyar bunƙasa harkokin dimokuraɗiya ta CDD.
Taron da aka gudanar a Abuja babban birnin Najeriya, ya samu halartar masu neman kujerar shugaban kasa irinsu ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi; Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP da Kola Abiola na PRP.
Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da Bola Tinubu na APC da ake gani a matsayin manyan ‘yan takarar ba su halarci muhawarar ba, amma Atiku ya tura mai yi masa takarar mataimaki, gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa domin ya wakilce shi.
Sai dai magoya bayan, LP da NNPP da PRP sun yi ta nuna rashin jin dadinsu da kuma caccakar Atiku da Tinubu bisa rashin zuwansu taron suna masu cewa Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Labaraba ake gane ta.
Suna dai ganin wannan muhawara ce ta masu neman kujerar shugaban kasa don haka babu wanda yake da ikon aike wani ko kauracewa taron da sunan wani uzuri na gangamin yaƘin neman zaɓe.
Yadda aka soma muhawarar
Kafin soma muhawarar magoya-baya da ‘yan kallo sun rinƙa ta maganganu suna ihu kan kauracewa taron da manyan ‘yan takarar na APC da PDP suka yi, batun da ya haifar da tsaiko wajen soma taron kan lokaci.
Sai dai daga bisani na shawo kansu, sannan aka shiga tattauna batutuwan da suka ja hankali da daɗaɗa zukatun wasu.
Haka zalika a shafukan sada zumunta an yi ta tsokaci tun daga farkon muhawarar har karshenta.
Kalaman Atiku daga bakin Okowa
A lokacin da yake tsokaci kan shirye-shiryensu kan batun tsaro a Najeriya, wakilin Atiku a taron, Ifeanyi Okowa ya ce Atiku ya yarda da batun tattara bayanan sirri da musayar bayanai tsakanin hukumomin tsaro.
Sannan ya ce akwai bukatar kafa ‘yan sanda jihohi, yana mai jaddada cewa yanayin da ake ciki a yanzu, jami’an tsaron tarayya su kaɗai ba za su iya bai wa ƙasar tsaro ba.
Ya ce suna fatan samar da nasu tsarin da tabbas zai taimaka domin za su yi amfani da mutanen da ke da karfin sanin yankinsu, da kuma dabarun samar da tsaro.
Don haka a ganinsu tsarin ‘yan sanda da ake amfani da su a wannan lokaci ba zai fitar da ƙasar daga matsalolinta ba.
Sannan ya yi tsokaci kan batun rawar da kamfanoni masu zaman kansu za su taka wajen samar da ci-gaba ta hanyar haɗa kan ‘yan kasa da jan ragamarta zuwa ga ci-gaba.
Ya ce Atiku, fitaccen ɗan kasuwa ne wanda kuma ke tafiyar da harkokin ilimi. Kwarewarsa a wadannan fanoni na kasuwanci da harkar samar da ilimi da masana’antu na sake tabbatarwa ‘yan Najeriya da cancantarsa na zama shugaban kasa.
Sannan ya tunasanar da ‘yan kasa yadda tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku, suka yi gwagwarmayar ragewa da ganin an yafe wa Najeriya basukanta.
‘Yan Obi sun yi gugar-zana
Magoya-bayan Peter Obi da suka yi fice a shafukan sada zumunta sun yi ta mayar da martani da jinjinawa ɗan takararsu.
Duk da cewa suna ganin akwai rashin dacewa Atiku da Tinubu su kauracewa taron. Mutumin da suke goyawa-baya ya faranta musu.
Peter Obi ya ce inda shi ke kan mulki a wannan lokaci da tuni ya ceto mutanen da ake garkuwa da su, yana mai bayyana raunin gwamnati mai ci wajen tafiyar da harkokin tsaro.
Obi ya ce da zai fitar da tsari mafi dacewa da nuna tausayi ga iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su.
Sannan ya ce ana iya rage matsalolin tsaro ko daƙileta baki ɗaya idan aka yi kokari ko mayar da hankali wajen fitar da mutane daga talauci.
Da aka yi masa tambaya kan batun me zai yi domin shawo kan rashawa, sai ya ce "na sha nanata cewa suna yin abin da suke so har a samu mutanen da ke azurta kan su a gwamnati sama da ‘yan kasuwa.
"Na shafe shekara 8 a mulki kuma babu wanda ya taɓa ji ko ganin na karɓo rance. Babu wanda ya taba gayyata ta ko ya yi korafi kan ɓatawar kuɗi.
"Wadannan su ne irin misalai da ke nuna cewa ba zan lamunci rashawa ko almubazaranci da dukiyar gwamnati ba karkashin ikona," in ji Obi.
Kwankwaso ya ci kasuwarsa
Sanye da kwat ɗinsa ɗan takarar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna bajinta domin ya ja hankali mutane da irin kalmomi da lafuza da ya yi amfani da su wajen amsa tambayoyin da ake masa, da kuma bayyana manufofinsa.
Sanata Kwankwaso a lokacin da yake tsokanci kan matsalolin tsaro, ya bada misali da mulkin Olusegun obasanjo, da yake rike da mukamin ministan, irin rawar da ya taka wajen tabbatar da tsaro a faɗin Najeriya da ma wasu ƙasashen Afirka.
Ya tunasar da tsare-tsaren da ya kawo da irin kuɗaɗen da suka yi amfani da su da ƙarin dakaru wajen tsaron Najeriya.
Ya ce ya alƙawarta inganta tsaron kasa ta hanyar karfafa gwiwar matasa su shiga aikin soji da sauran ayyukan tsaro.
Ya ce abin kunya ne a ce a wannan zamanin, jami’an tsaro sun gaggara gano maboyar ‘yan ta’adda, musamman a wannan lokaci da komai ake so ayi sai da wayar sadarwa, wanda sanin kowane ba abu ne mai wahala gano mutum ta waya ba.
Sanata Kwankwaso, wanda tsohon gwamna ne a Kano, ya ce yana baƙin cikin ganin yanayin da ake ciki a Najeriya kamar kowanne ɗan kasa, wannan dalili ne ya sanya suka rinka sauya sheka daga PDP zuwa APC a kokarin neman mafita.
Sannan a lokacin da yake amsa tambaya kan batun addini da kabilar wasu ‘yan takara, Kwankwaso ya ce, "Kundin tsarin mulkin Najeriya ya fayyace komai akan wannan batu. Don haka duk wani wanda zai fito yana magana a kan ƙabilanci ko yare ko addini ko yanki to ya faɗi zaɓe tun kafin ranar zaɓen.
Sannan ya ja hankalin cewa Arewa ba za ta iya cin zaɓe ba tare da Kudu ba, hakazalika ita ma Kudu sai da Arewa.
Ya kuma ce babu laifi idan uzuri mai karfi ya hana wani ɗan takarar halarta taron, muddin yana da wakilci.
Sai dai hakan ba wai kuma yana nufin wani ɗan takarar ya fito yana tinkahon cewa zabgoggi ba su ba shi damar halartar irin wannan muhawara ba baki ɗaya.
Don haka mutum irin Okowa ya fi wanda ya gaggara tura wakilci, a cewarsa.
Me ɗan takarar PRP ya ce?
Kola Abiola ya ce shi idan aka zaɓe shi, ba zai yi tashi tafiyar da tsoffin kusoshin gwamnati ba, da sake dawo da ‘yan siyasar da ake ganin suna tattare da gazawa. Shi sabon zubi zai yi.
Ya bayyana kansa a matsayin sabon shiga wanda bai taɓa riƙe wani ofishin gwamnatin Najeriya ba, Don haka shi ne mafi dacewa da wannan aiki.
Ya ce hanayensa a tsaftace suke ba sa dauke da kowanne irin tarkacen tsoffin gwamnatoci ko wata jam’iyya.
"Muna son amfani da wannan dama wajen juya akalar Najeriya da yiwa ‘yan kasa gwagwarmaya."
Ya ce Najeriya ba ta mutum guda ba ce, ko ta wasu rukunni mutane kalilan.
"Najeriya kasa ce ta kowa, kuma kowa na da ‘yanci neman kowane irin kujera, ba wai a rinka ɗanwaken zageye ba.
"Ana bukatar sabbin jini da fuskoki masu hikima da basira da kwazo", in ji Kola Biola.
Kola ya ce shi ne mafi dacewa domin yana tattare da dabarun shawo kan matsalolin tsaro da inganta tattalin arzikin kasa.
Martanin Tinubu
Kwamitin yaƙin neman zaɓen APC, sun kare ɗan takararsu, Bola Ahmed Tinubu, suna mai cewa taron ya yi karo ne da wasu muhimman ayyukansa.
Kwamitin ya kuma ƙi yarda da cewa ya kamata a ce ya tura wakilci ko kuma ya bada hujja mai karfi kan kauracewa taron muhawarar.
Me ‘yan Najeriya ke cewa?
‘Yan Najeriya dai musamman a shafukan sada zumunta sun yi ta mayar da martani, da alla-wadai da kin halartar ɗan takarar APC wannan muhawara.
Galibi a shafin Twitter da Facebook sun rinka yabawa Kwankwaso da yanko wasu kalamansa suna ma sa jinjina.
Hakazalika akwai masu cewa Peter Obi ya burge su.
@lordleomax ya ce: Ya aka yi muka tsallake @kwankwasoRM kuma zabo Bubu a matsayin shugaba. Arewa me ya sa??? Me ya sa aka boye Kwankwaso aka ba mu Bubu. Wannan mutumin ya kamata a ce yana cikin wannan tafiya ta CIC shekaru 7 baya.
@ifeaboyeji Ta ce; Abokiyar zamata na mun tambayar ko Kwankwaso shugaban kasa ne. Ko kuwa dai ta hango alkibila ne?
@Makavelli275 Ya ce; Ku bi a hankali kan batun kwankwason nan, babu wani abu sabo a kansa, shi ya ire-iren 'yan siyasar nan ne da muke son kawarwa. A dage daga hankali a kansa. Bai cancanci wannan tallatawa kyauta ba. Aike Obi Aso Rock, shi muka sanya a gaba.
@aderopoafo ya ce; Abin takaici ne ganin cewa tafiyar Kwankwaso da Obi ba za ta kai labari ba. Alhaji Rabiu yana da ilimi da kwazo, sannan ga shi yana da cancanta. Zan ci-gaba da girmama tafiyar Kwankwasiyya..