Man United ta doke Lens a wasan sada zumunta

An wallafa

Marcus Rashford ya taka rawar gani yayin da Manchester United ta yi nasara da ci 3-1 a wasan sada zumunta da kungiyar ta buga da kungiyar Lens a Old Trafford.

Duk da cewa Lens ta fara zura kwallo a raga bayan Andre Onana ya yi sake kwallo ta wuce shi daga tsakiyar fili, Rashford ya farke kafin Anthony ya jefa wa United kwallo ta biyu.

An gabatar da sabon dan wasa Rasmus Hojlund ga 'yan kallo 57,802 kafin a fara wasan amma Rashford ya nuna cewa United na da dan wasan gaba mai hazaka.

A ranar Lahadi ne ƙungiyar za ta kammala atisayen tunkarar kakar wasa ta bana da Athletic Bilbao a birnin Dublin.