Liverpool ta sayi Endo daga Stuttgart

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta kammala sayen dan wasan tsakiya Wataru Endo daga Stuttgart kan kudi kusan Yuro miliyan 19.
Dan wasan na Japan mai shekaru 30 ya amince da kwantiragin shekaru hudu.
Liverpool ta dauko Endo ne bayan ta rasa dan wasan Ecuador Moises Caicedo da dan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia zuwa Chelsea.
Endo na iya taka leda a matsayin mai tsaron baya amma Liverpool ta dauko shi ne a matsayin dan wasan tsakiya.
Dauko Endo - wanda shi ne kyaftin din tawagar kasar Japan da Stuttgart -na zuwa ne bayan ficewar tsofoffin 'yan wasan tsakiya na Reds Fabinho da Jordan Henderson da James Milner da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain a bazara.
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya riga ya karfafa tsakiyar filin tawagarsa, inda ya dauko Alexis MacAllister da Dominik Szoboszlai wadanda suka fara wasa a karshen mako da Chelsea a Stamford Bridge.







