Za a gina sabon filin wasa na Man United - Ratcliffe

Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wanda ya mallaki wani kaso na hannun jarin ƙungiyar Manchester United, Sir Jim Ratcliffe ya ce yana fatan zai gina sabon filin wasa da arewacin Ingila zai ke mora.

United tana wasa a Old Trafford mai cin ƴan kallo 74,310 tun daga 1910, Ratliffe na ganin filin ya gaji ana buƙatar sabon wuri.

Za a iya gina sabon filin wasan kusa da Trafford Park.

Ratcliffe ya yi karin bayani kan sabon filin da za a gina da zai riƙa karɓar bakuncin wasannin tawagar Ingila da FA Cup da wasan ƙarshe a Champions League da kodayaushe ake yi a Wembley.

Ba a zaɓi filin Old Trafford da za a kara a gasar cin kofin nahiyar Turai ba wato Euro 2028, rabon da ya karɓi baƙuncin wani babban wasa tun karawar ƙarshe a Champions League a 2003, inda AC Milan ta ci Juventus a bugun fenariti.

Ratciffe, mai shekara 71, wanda aka haifa a Manchester ya kammala mallakar wani hannun jarin ƙungiyar ranar Litinin da ya kai fam biliyan 1.25.

Cikin ƙunshin kwantiragin da aka ƙulla zai samar da fam miliyan 237 don bunƙasa ƙungiyar da kuma filin wasa.