'Yadda na rasa hannuna ɗaya a wurin rabon faɗa'

Salisu na ƙoƙarin raba faɗa ne sai aka sare shi

Asalin hoton, OTHER

    • Marubuci, Mansur Abubakar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Kano
  • An wallafa

Salisu mai shekara 23, mazaunin birnin Kano na ɗaya daga cikin waɗanda ba za su taɓa mantawa da shekarar 2022 ba, saboda abin da ya faru da shi lokacin rabon faɗa.

A wata rana bayan ya taso daga aiki, Salisu ya yi ƙoƙarin sulhunta wasu mutane biyu da ke faɗa, sai dai bai san shi ne wanda zai fi dukkanin su jin jiki ba.

Ya shaida wa BBC cewa "na tashi a ranar cikin farin ciki, sai dai ban san cewa a ranar ce zan haɗu da tsautsayin da zai sauya min rayuwa ba, har abada."

"Bayan na kwashe wunin ranar a shagon ɗinki, na tashi da misalin ƙarfe 9 na dare, inda na bi ogana domin kai wani aiki da muka yi, daga nan sai na kama hanyar gida."

"Daga nan sai na tsaya na sayi abinci, sannan na zauna a wani wuri kusa da gida domin na ci abinci, a wurin ne wani abokina ya ke koka min kan wani yaro da ke yi masa barazana."

Bayan lokaci kaɗan sai Salisu ya miƙe tsaye domin sulhunta wasu matasa biyu da ke cacar baki.

Lokacin da na fara masu magana sai ɗaya daga cikin su ya zaro wuƙa yana so ya caka min, inda ya same ni a hannu, sai jini ya fara zuba."

Daga nan ne faɗa ya ƙare, shi kuma wanda ya caka wuƙar ya tsere, duk da dai daga baya jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama shi.

Jinya a asibiti

"Daga nan ne aka garzaya da ni asibitin Murtala inda na kwashe kwana uku ana kula da ni."

Salisu ya ce daga nan ne aka tura shi asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano, inda su ma suka tura shi zuwa asibitin ƙashi na Dala.

...

Asalin hoton, OTHER

"A asibitin Dala aka ce mana dole sai an yanke hannun domin jijiyoyin da suke kai wa hannun jini sun tsinke."

"Na yi kuka iayakar kuka saboda tunanin yadda rayuwata za ta sauya."

"Na iya ɗinki sosai, amma yanzy ba zan iya ba, daga ƙoƙarin yin taimako."

Salisu bayan an yanke masa hannu

Asalin hoton, OTHER

Ƙarshen sana'ar ɗinki

Salisu ya ce a yanzu baya yin komai saboda ba zai iya aiki da hannu ɗaya ba.

"Yanzu ina zaune ne a gida tare da iyalina, waɗanda su ne ke taimaka mini suna ƙarfafa min gwiwa."

An tambaye shi ko zai so a yi masa hannun roba wanda zai taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa, sai ya ce likitoci sun ce hakan zai yi wuya, domin an yanke hannun da yawa.

Salisu a lokacin da ake dinki

Asalin hoton, OTHER

'Ba zan bai wa mutane shawarar su daina raba faɗa ba'

Salisu ya ce duk da abin da ya faru da shi ba zai bai wa mutane shawarar su daina raba faɗa ba idan suka ga ana yi.

"Na ɗauki abin da ya faru da ni a matsayin kaddara daga Allah, ko a gobe na ga wasu suna faɗa zan raba su, domin abin da ya kamata mutanen kirki su rinƙa yi ke nan."

"Saboda haka ba zan shawarci mutane su daina raba faɗa ba saboda tsoron wani abu ya faru da su."

Tuni dai kotu ta yanke wa wanda ya yanki Salisu da wuƙa hukuncin ɗauri, inda yanzu haka yake zaman kaso a gidan gyara hali na Kurmawa da ke jihar Kano.

Salisu tare da iyalinsa

Asalin hoton, OTHER